✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan tawaye sun kashe mutum 50 a Burkina Faso

Yankin dai na zaman filin daga tsakanin gwamnati da ’yan tawaye

Akalla mutane 50 ne suka mutu a wani harin da ’yan tawaye suka kai wani kauye da ke Arewacin Burkina Faso.

Kakakin Gwamnatin kasar, Lionel Bilgo ya rawaito cewa maharan sun far wa kauyen mai suna Seytemga Commune tsakanin ranakun Asabar da Lahadin da suka gabata.

Yankin dai na kan iyaka da inda wasu mayaka da ake kyautata zaton na Al-Qa’ida da ISIS ne suka mamaye.

“Sojoji sun gano gawarwaki 50 bayan harin kauyen Seytenga, kuma har yanzu muna kan bincike,” inji Lionel Bilgo.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta yi Allah-wadai da harin, tare da kiran gwamnati da ta dau matakin da ya da ce kan wadanda suka kai shi.

Seytenga dai ya zamo filin luguden wuta tsakanin gwamnati da ’yan tawaye a makon da ya gabata.

Rahotanni na nuna cewa hatta ’yan sanda sai da aka samu gawarsu, wanda hakan ne ya sanya sai da sojoji suka sanya hannu har suka kama mayakan ’yan tawayen kimanin 40.