✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan tawaye sun kashe sojoji 4 a Senegal

’Yan tawaye sun kashe sojojin Senegal hudu tare da yin garkuwa da wasu bakwai a wani rikici da ya barke tsakanin bangarorin biyu a kan…

’Yan tawaye sun kashe sojojin Senegal hudu tare da yin garkuwa da wasu bakwai a wani rikici da ya barke tsakanin bangarorin biyu a kan iyakar kasar da Gambia.

Wata majiyar tsaron kasar ta ce lamarin ya auku ne a makon da ya gabata, yayin da rikici ya kaure tsakanin jami’an sojin Senegal da ’yan tawayen MFDC, sojoji 3 suka mutu, sannan kwanaki  bayan faruwar lamarin na hudun ya kwanta dama bayan jinyar da ya yi daga raunin da ya samu a rikicin.

Majiyar sojin Senegal ta kuma ce a halin yanzu ’yan tawayen MFDC (Movement of Democratic Forces of Casamance) na rike da jami’an sojinta 7, kuma dukanninsu na cikin koshin lafiya.

Kungiyar ta MFDC ke da alhakin rikicin da ya barke a shekarar 1982 a yankin kudancin Senegal, wanda ya yi sanadiyar hasarar dubban rayuka.

A sanarwar farko da majiyar ta fitar, ta ce sojinta biyu aka kashe tare da tsare wasu 9, kuma babu wanda ya bace, toh saidai bayan tabbatar da sahihin adadin wadanda lamarin ya rutsa da su, ta sake fitar da sabuwar sanarwar dake bayyana halin da ake ciki a yanzu.

Wadannan sojin dai na daga cikin jami’an da Kungiyar ECOWAS ta tura Gambia domin wanzar da zaman lafiya a shekarar 2017, daidai lokacin da tsohon Shugaban Kasar Yahya Jameh ya ki sauka daga kan mulki duk kuwa da cewa ya fadi zabe, jami’an da aka fi sani da suna ECOMIG.