✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan tawayen Ambazoniya sun kashe sarki da mutum 11 a Taraba

Mutane na kaura daga yankin bayan harin ’yan tawayen Anbazoniya daga Kamarum.

Sojojin ’yan tawaye masu neman kafa kasar Ambazoniya daga kasar Kamaru sun halaka wani basarake da mutum 11 a garin Manga da ke kan iyakan Najeriya da Kamaru a Jihar Taraba.

Mazauna yankin sun fara kaura domin tsira da rayuwarsu ne bayan sojojin sa-kai sun mamaye garin na Manga wanda ke cikin Karamar Hukumar Takum a ranar Laraba suka yi wa mutane luguden wuta.

Shugaban Karamar Hukumar Takum, Mista Tikari, ya bayyana cewa an gano gawarwaki biyar daga cikin wadanda aka kashe kuma al’ummar yankin duk sun kaurace wa gidajensu.

Ya ce an tura sojoji daga barikin sojoji dake garin Takum domin kare rayukan mazauna kan iyakan Najeriya da Kamaru da a karamar hukumar.

A watan jiya ma sojojin kasar Kamaru sun afka wa wasu garuruwa uku da ke Karamar Hukumar Kurmi a jihar ta Taraba inda suka kona gidaje da wuraren kasuwanci.