✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan wasa 10 da ke takarar gwarzon dan kwallon Afirka na 2022

Babu dan Najeriya ko daya a cikin jerin da CAF ta fitar.

Hukumar kwallon kafa ta Afirka CAF, ta fitar da jerin ’yan wasa goma da ke takarar gwarzon dan kwallon Afirka na 2022.

Za a bayyana gwarzon bana a Rabar a Morocco ranar 21 ga watan Yulin 2022.

Cikin goman da Hukumar CAF ta sanar sun hada da mai rike da kyautar, Sadio Mane (Senegal da Bayern Munich) da wanda ya taba lashe kyautar Riyad Mahrez (Algeria da Manchester City) da Mohamed Salah (Masar da Liverpool).

A bana ma dai lamarin bai zo wa Najeriya da sa’a ba, inda babu dan wasan tawagar Super Eagles ko daya da ya samu shiga jerin hazikan ’yan wasan da Hukumar Kwallon Kafar Afirkar ta fitar ba.

Lokacin da aka fitar da jerin sunayen farko, ‘yan wasan Super Eagles da suka hada da Moses Simon da Akinkunmi Amoo ne suka shiga jerin, amma daga bisani aka cire sunayensu bayan an yi tankade da rairaya.

Sau biyar kacal ne a tarihi aka samu wani dan wasan Najeriya ya lashe kyautar gwarzon CAF na shekara, inda Emmanuel Amuneke ya kasance na farko da ya taba lashewa a shekarar 1994, sannan Kanu Nwankwo ya lashe kyautar a shekarar 1996.

Bayan shekara daya kuma Victor Ikpeba ya zama gwarzon dan wasan shekaara na CAF, kafin Kanu ya sake karbe kambun bayan shekaru biyu.

Ga jerin ‘yan wasan Afirka 10 da ke takarar gwarzon dan kwallon CAF na 2022:

Riyad Mahrez (Algeria da Manchester City)

Karl Toko Ekambi (Kamaru da Olympique Lyonnais)

Vincent Aboubacar (Kamaru da Al Nassr)

Sebastien Haller ( Kwaddebuwa da Ajax)

Mohamed Salah (Masar da Liverpool)

Naby Keita (Guinea da Liverpool)

Achraf Hakimi (Morocco da Paris Saint-Germain)

Edouard Mendy (Senegal da Chelsea)

Kalidou Koulibaly (Senegal da Napoli)

Sadio Mane (Senegal da Bayern Munich)