✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan wasa 5 da Manchester United ke son saya a Janairu

Kungiyar Manchester United ta shirya tsaf don sake yi wa kanta garambawul

Tun bayan sallamar Ole Solskjaer a matsayin koci tare da nada Ralf Rangnick a matsayin kocin wucin gadi, kungiyar da Manchester United ta shirya yin garambawul.

Tuni Rangnick ya nuna sha’awarsa na daukar wasu ’yan wasa a watan Janairu don kai kungiyar ga gaci.

Ga jerin sunayen ’yan wasan da United ke son dauka:

  1.  Declan Rice: Dan wasan tsakiya ne da ke taka leda a West Ham, kuma tuni Manchester United ta nuna sha’awarta ta daukar sa a watan Janairu.
  2. Kalvin Phillips: Dan asalin kasar Birtaniya da ke taka leda a Leeds United. Sabon kocin Manchester United na son daukar sa don hada shi da Rice a tsakiyar fili.
  3. Amadou Haidara: Rangnick ya taka rawa wajen kawo dan wasan zuwa kungiyar Red Bull Salzburg a 2019, kuma yanzu yana son sake horar da dan wasan a Manchester United. Tuni ya bayyana wa masu ruwa da tsaki na kungiyar sha’awarsa ta sake yin aiki da dan wasan.
  4. Kieran Trippier: Manchester United ta jima tana son sayen dan wasan, wanda dan asalin Birtaniya ne amma ba ta cimma yarjejeniya da Atletico Madrid ba a karshen kakar wasanni. Amma Untied na son gwada sa’arta a watan Janairu don dauko dan wasan zuwa Old Trafford.
  5. Jules Kounde: Dan wasan bayan Sevilla na daga cikin ’yan wasan da manyan kungiyoyi suka so dauka a karshen kakar wasanni, amma daga karshe bai je kowace kungiya ba. Rangnick na son sayen dan bayan ne don hada shi da Varane, tsohon dan wasan bayan Real Madrid.