✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan wasan Firimiyar Ingila 5 sun kamu da Coronavirus

Tuni ’yan wasan biyar sabbin kamuwa da cutar suka killace kansu.

Hukumar da ke sa ido kan gudanar da gasar Firimiyar Ingila, ta sanar da cewa an samu karin ‘yan wasa biyar da suka kamu da kwayoyin cutar coronavirus bayan gwajin gano masu cutar da aka gudanar daga ranar 5 zuwa 11 ga watan Oktoban 2020.

Sanarwar da Hukumar ta fitar ranar Litinin a shafinta na yanar gizo, ta ce an yi gwajin gano masu dauke da kwayoyin cutar a kan ’yan wasa dubu 1 da 128 da ke buga tamola a kungiyoyin Firamiyar Ingila cikin kwanaki shida.

Cikin wani rahoto da jaridar RFI Hausa ta wallafa ya ce, tuni ’yan wasan biyar sabbin kamuwa da cutar suka killace kansu, inda za su kasance a ware na tsawon kwanaki goma domin gudun yada cutar ga wasu.

Sai dai sanarwar ba ta bayyana sunayen ’yan wasan biyar ba da suka kamu da cutar a baya bayan nan.

Da yiwuwar ‘yan wasan Ingila, Ben Chilwell na kungiyar Chelsea da Kieran Trippier na kungiyar Atlético Madrid, na cikin jerin ’yan wasan da suka kamu, a yayin da aka zare sunayensu daga cikin tawagar Ingila da za ta fafata da tawagar kasar Denmark a gasar Kofin Zakarun Turai na kasashe wato Nations League.

Sakamakon gwajin da Hukumar Firimiyar ta Ingila ta yi wa ’yan wasa a tsakanin ranar 28 zuwa 4 ga watan Oktoban bana, ya nuna cewa an samu ‘yan wasa 9 da suka kamu da cutar ciki har da ‘yan wasan kungiyar Liverpool uku – Sadio Mane da Naby Keita da Thiago Alcantara.