✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yanayin fitowar jama’a a zaben kananan hukumomin Kano

Mutane ba su fito sosai ba a kwaryar birni, amma sun yaba da yanayin zaben

An samu karancin fitowar masu kada kuri’a a Zaben Kananan Hukumomin Jihar Kano da aka gudanar ranar Asabar 16 ga Janairu, 2021.

Kamfanin Dillalncin Labaru na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa jama’a ba su fito sosai ba a kusan daukacin rumfunan zaben da wakilansa suka zagaya a kwaryar birnin Kano.

Unguwannnin sun hada da Chedi, Zage, Zango, Gandu, Sharada, Wailawa, Dorayi, Kabuga da kuma Rijiyar Zaki a Kananan Hukumomin Birni, Gwale, da kuma Ungogo.

Rahoton ya nuna an fara zaben ne da misalin karfe 10:30 na safe cikin  tsauraran matakan tsaro na ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro.

Masu kada kuri’a sun yaba da zaben Kano

Sai dai wasu masu zaben da aka zanta da su sun bayyana farin cikinsu da shiga zaben.

Malam Jazuli Yusuf a Karamar Hukumar Gwale ya ce ya kada kuri’arsa a a zaben ne domin tabbatar da ’yancinsa.

Shi kuma Yusuf ya ce shiga zaben zai ba wa jama’a damar zabar shugabannin da suke so su jagorance su a matakin karamar hukuma.

Amina Isa, a unguwar Zage, ta yaba da zaben da kuma yadda mutanen da suka fito suka kasance cikin lumana.

Firdausi Dahiru Abubakar ta ce ta fito zaben ne domin ganin ba a bar mata a baya ba a zaben.

Ta kuma bayyana fatarta cewa zaben sai kawo kyakkyawan sauyi ta bangaren samar da ingantaccen ilimi da lafiya da sauransu.

Jam’iyyu 12 ne suka tsayar da ’yan takara a zaben a fadin Kananan Hukumomi 44 na Jihar Kano.

Hukumar Zabe ta Jihar Kano (KANSIEC) ta ce zaben ya hada da na Shugabannin Kananan Hukumomi 44 da Kansiloli 484 a fadin jihar.

KANSIEC ta ce ta tura jami’ai 48,000 zuwa ga rumfunan zaben 11,500, da kuma jami’an tsaro 10,000 domin tabbatar da gudanar da sahihin zabe.