✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yanke albashi: ASUU ta kira taron gaggawa

Kungiyar ASUU za ta yi zaman gaggawa ranar Litinin don yanke shawara kan sake tsunduma yajin aiki.

Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU) ta kira zaman gaggawa na Majalisar Zartarwarta don yanke shawara kan shiga sabon yajin aiki.

ASUU ta kiran zaman gaggawan ne sakamakon rabin albashin watan Oktoba da Gwamnatin Tarayya ta biya malaman jami’a bayan sun janye yajin aiki.

Wani mamba a kwamitin zartarwar ASUU ya ce mambobin kungiyar sun fusata da yanke albashin nasu da suke zargin Ministan Kwadago, Chris Ngige ya yi.

Wani jami’in kungiyar ya shaida wa wakilinmu cewa majiya mai tushe ce ta sanar da su cewa ministan ne ya ba da umarnin yanke albashin da aka biya su a Oktoba.

“Ina tabbatar maka cewa NEC din ASUU NEC zai yi zama ranar Litinin 7 ga Nuwamba domin daukar matsaya game da shiga sabon yajin aiki, saboda rabin albashin da aka biya mu a Oktoba.

“Rassann kungiyar sun fusata da abin da Gwamnatin Tarayya ta yi, don haka kungiyar za ta yanke shawara a ranar 7 ga watan Nuwamba,” in ji shi ta wayar tarho.

Wakilimu ya yi kokarin samun shugaban kungiyar, Farfesa Emmanuel Osodeke domin sammun karin haske, sai dai wayarsa ba ta shiga.

Amma a martaninsa, Ngige, ya ce zargin malaman ba shi da tushe.

Ya bayyana cewa babu wanda ya yanke musu albashi ko biyan su rabi.

Ya kara da ceaw an biya su ne na  iya kwanakin da suka yi aiki a watan Oktoba, domin ba wanda zai biya su ladar aikin da ba su yi ba.