✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yanke wa mutane Lantarki ba tare da ba su gargadin kwana 10 ba saba wa doka – FCCPC

Hukumar Kula da Gasa da Kare Hakkin Masu Sayen Kaya ta Kasa (FCCPC) ta ce yanke wutar lantarkin mutanen da ba su biya kudi ba…

Hukumar Kula da Gasa da Kare Hakkin Masu Sayen Kaya ta Kasa (FCCPC) ta ce yanke wutar lantarkin mutanen da ba su biya kudi ba ba tare da ba su gargadin kwana 10 ba da kamfanonin rarraba wutar lantarki ke yi ya saba wa doka a Najeriya.

Mataimakin Shugaban Hukumar, Babatunde Irukera, ne ya bayyana hakan ranar Laraba a jihar Kuros Ruba, a wani zauren warware korafin masu amfani da wutar lantarki da hukumar ta shirya.

Irukera ya kuma koka kan yadda Kamfanin Rarraba Hasken Wutar Lantraki ta Fatakwal (PHEDC) ba ya gudanar da ayyukansa yadda ta kamata, inda ya ce bincikensu ya gano ba sa tabuka abin-a-zo-a-gani musamman ma wajen karbar kudin wutar daga mutane.

Ya kuma ce sun samu korafe-korafe daga mutane da dama kan yadda su ke datse musu wutar ba tare da bin ka’idojin da dokar kasa ta shimfida musu ba.

“Ina son sanar da ku cewa al’ummar jihar Kuros Ruba ba sa jin dadin yadda kuke gudanar da aikinku, ciki kuwa har da Gwamnan jihar, kuma sun ce da son ransu ne ma kamfaninku na PHEDC ba zai ci gaba da aiki a jiharsu ba.

“Datse wutar mutane da kuke yi ba kakkautawa ba wai ya saba wa doka ba ne kadai, cin zarafi ne ga hakkin ’yan kasa, balle a je ga na datse na unguwa guda kuma.

“Wasu daga cikin ’yan unguwar nan na biyan kudin wuta, don haka yanke ta kowa da kowa rashin adalci ne babba,” inji Mataimakin Shugaban na FCCPC.

“Haka kuma, duk kasuwancin da ya gaza gamsar da wadanda yake yi dominsu, sannan yake tilasta mutane su biya kudin wuta ba tare da ya ba su wutar ba, ko da kuwa don wani abu ya lalace ne daga sama, ya saba wa kundin dokar Najeriya,” inji Irukera.

Ya kuma koka kan yadda Kamfanin ke kin sayen na’urorin rarraba lantarkin a unguwannin mutane idan sun samu matsala, har sai sun sanya kudinsu sun saya, kuma karshe PHEDCn su karbe iko da ita.