Yanzu APC na da mambobi miliyan 40 a Najeriya – Buni | Aminiya

Yanzu APC na da mambobi miliyan 40 a Najeriya – Buni

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni
    Baba Martins da Sani Ibrahim Paki

Shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC na kasa kuma Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya ce yanzu haka jam’iyyarsu na da mambobi akalla miliyan 40 a Najeriya.

Ya ce sun tattara alkaluman ne bayan kammala aikin sake rajistan mambobin jam’iyyar da aka gudanar a kwanakin baya.

Kazalika, Gwamnan ya kuma sanar da 26 ga watan Fabrairun 2022 a matsayin ranar babban taron jam’iyyar.

Ya sanar da haka ne ranar Talata, yayin taron mata na jam’iyyar da ke gudana a Abuja.

Gwamnan ya yi kira ga matan da su fito kwansu da kwarkwata a fafata da su a babban taron da ke tafe ta hanyar tsayawa takara.

Mai Mala ya kuma ce jam’iyyarsu a shirye take tsaf ta lashe babban zaben kakar 2023 da ke tafe.