✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnonin Arewa ta Tsakiya na ganawa a fadar Aso Rock

Gwamnonin jihohin Arewa ta tsakiya a Najeriya na yin wata ganawa yanzu haka da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa Ibrahim Gambari a fadar gwamnati ta…

Gwamnonin jihohin Arewa ta tsakiya a Najeriya na yin wata ganawa yanzu haka da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa Ibrahim Gambari a fadar gwamnati ta Aso Rock.

Gwamnan Kogi, Yahaya Bello da takwaransa na jihar Neja Sani Bello da gwamnan Kwara Abdulhahman Abdulrazak na halartar taron. Sauran gwamnonin su ne  Abdullahi Sule na jihar Nasarawa da kuma gwamnan Filato Simon Lalong, a fadar Aso Rock.

Babu bayani game rashin ganin gwamnan Benue, Samuel Ortom, wanda shi ne kadai wanda ba dan jam’iyyar APC ba daga yankin na Arewa ta tsakiya.

Jihohin Neja da Nasarawa da Benue su ne suka fi fama da matsalar tsaro da suka hada da ‘yan bindiga da rikicin kabilanci. Kazalika jihar Filato inda a baya-bayan nan abin ya yi sauki.

Babu dai tabbaci game da hakikakin maudu’in da gwmanonin ke tattauna da Gambari.