✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yanzu Najeriya ce kasar da kungiyar IS ta fi kai wa hari a duniya – Rahoto

Wannan dai shi ne karon farko da wata kasa ta zarce Iraqi tun bayan kafa kungiyar

Wani sabon rahoto ya nuna cewa yanzu haka Najeriya ta zarce kasar Iraqi a yawan hare-haren da kungiyar IS ko ISWAP ke kai wa kowacce kasa a fadin duniya.

Rahoton, wanda wata cibiya da ke sa ido kan ayyukan ta’addanci a duniya mai suna Jihad Analytics ta fitar, ya yi nazarin kasashen da kungiyar ta fi kai wa hare-hare a duniya daga farkon watan Janairun shekarar 2022 zuwa watan Afrilu.

A cewar rahoton, reshen kungiyar na Afirka ta Yamma da aka fi sani da ISWAP, ya kai hare-hare har sau 162, sabanin sau 120 da ya kai kasar Iraqi, wacce aka wa kallon ita ce cibiyar kungiyar.

Wannan ne dai karo na farko da aka samu wata kasa ta zarce Iraqi a yawan hare-haren tun lokacin da aka kirkiri kungiyar.

Kazalika, rahoton ya nuna fiye da rabin hare-haren an kai su ne a kasashen Afirka.

Ragowar kasashen da kungiyar ta fi kaddamar da hare-haren sun hada da Siriya (sau 77) da Afghanistan (45) da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango (37) Mozambique (20) sai kuma Masar mai 16.

Sauran su ne Mali mai 11, Somaliya da Pakistan masu 10, Philippines mai biyar da Nijar da Kamaru masu uku-uku, sai Libya mai biyu da Isra’ila mai hari daya kacal.