✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yanzu zaben Amurka ya fi na kasashe masu tasowa lalacewa – Trump

Shugaban Trump ya ce zaben kasar ya fi na kasashe masu tasowa lalacewa.

Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce zaben da aka gudanar a ranar uku ga watan Nuwambar 2020 a kasar ya fi na kasashe masu tasowa lalacewa.

Shugaban ya bayyana hakan ne a wasu jerin sakonni da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Laraba inda ya kuma sake nuna kin amincewarsa da kayin da ya sha a hannun Joe Biden na jam’iyyar Democrat.

Biden dai ya sami kuri’u 306 na kwalejin zabe inda ya doke Trump wanda ya sami 232.

Yayin da Biden ya sami tarin kuri’u 81,283,485, shi kuwa Shugaba Trump kuri’u 74,233,744 ya samu.

“Ko a jiya sai da aka gano karin kuri’u 50,000. Wasu shashashai sun tozarta Amurka a idon duniya. Tsarin zabenmu a yanzu ya fi na kasashe masu tasowa lalacewa,” Trump ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Ko a ranar Laraba sai da Trump ya nanata kiransa ga mataimakinsa Mike Pence, da ya yi fatali da kuri’un da aka kada ba bisa ba zuwa jihohin da suka fito.

“Jihohi na so su yi wa kuri’unsu kwaskwarima wanda sun yarda da cewa an tafka magudi a cikinsu. Abinda kawai nake bukata Mike ya yi shine yin fatali da wadannan kuri’un zuwa jihohinsu, mu kuma mu lashe zabe. Ka aikata hakan Mike, wannan ne lokacin da ake bukatar jajircewa,” inji Trump.