✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yar Ayatollah Khamenei ta bukaci kasashe su yanke hulda da Iran

Malama Farideh wadda injiniya ce, mahaifinta fitaccen dan adawa ne a kasar.

’Ya ga Shugaban Addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, mai suna Farideh Moradkhani ta yi kira ga gwamnatocin kasashen duniya su yanke duk wata alaka da kasar Iran, saboda yadda take murkushe masu zanga-zangar da aka faro bayan mutuwar wata budurwa a hannun ’yan sanda.

A wani bidiyo, an ga Farideh Moradkhani wadda ’yar wata ’yar uwar Ayatollah Khamenei ce tana cewa, “Ya ku mutane masu ’yanci! Ku kasance tare da mu kuma ku gaya wa gwamnatocinku su daina goyon bayan wannan gwamnati mai kisa da kashe-kashen yara.”

Ta ci gaba da cewa wannan gwamnati ba ta biyayya ga ka’idojinta na addini kuma ba ta san wasu ka’idoji ba face tilastawa da kuma ci gaba da mulkin danniya.

Malama Farideh wadda injiniya ce, mahaifinta fitaccen dan adawa ne a kasar.

Har zuwa hada rahoton ofishin Ayatollah Ali Khamenei bai ce uffan a kan kiran nata ba, kuma Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya nemi jin ta bakin hukumomin qasar, amma sun ki cewa kala.

An ruwaito cewa a dalilin zanga-zangar da ta rikide zuwa rikici an kashe mutu 450 ciki har da kananan yara 63 a wata biyu da aka shafe ana tashe-tashen hankali a fadin Iran.

Sannan an kashe jami’an tsaro 60, kuma ana tsare da masu zanga-zangar 18,173.

Zanga-zangar ta samo asali ne sakamakon mutuwar Mahsa Amini wata budurwa mai kimanin shekara 22 a hannun jami’an tsaro, bayan kama ta kan zargin “Rashin sanya lullbi.”

Jalal Mahmoudzadeh dan Majalisar Dokoki daga birnin Mahabad na yankin Kurdawa ya bayyana a ranar Lahadin da ta gabata cewa an kashe kusan mutum 105 a yankunan da Kurdawa a zanga-zangar.

Yana magana ne a wata muhawara a Majalisar Dokokin kasar, kamar yadda shafin Intanet na Etekhan ya ruwaito.

Masu zanga-zanga daga sassan qasar sun ci gaba da kona hotunan Ayatollah Khamenei tare da kiran a kawar da gwamnatin kasar.

A ranar Juma’ar da ta gabata ce dan uwan Farideh, mai suna Mahmoud Moradkhani da ke zaune a kasar Faransa kuma x6aya daga cikin fitattun masu fafutikar kare hakkin al’ummar Iran, ya watsa bidiyon a shafinsa na Twitter, inda ya bayyana cewa an kama ’yar uwar tasa a yayin da ta bayyana a ofishin mai gabatar da kara a birnin Tehran a ranar 23 ga Nuwamba.

Mahmoud Moradkhani ya ce a farkon bana Ma’aikatar Leqen Asiri ta Iran ta kama Farideh, daga bisani kuma ta bayar da belinta.

Kamfanin Dillacin Labarai na HRANA ya ce tana cikin gidan yarin Evin na Tehran.

Moradkhani, ya ce tun farko ta fuskanci hukuncin daurin shekara 15 a gidan yari kan wasu tuhume-tuhume da ba a fayyace ba.

Mahaifinta, Ayatollah Ali Moradkhani Arangeh, malamin Shi’a ne da ya auri ’yar uwar Khamenei, kuma ya rasu a bay6abayan nan a birnin Tehran, bayan shafe shekaru da dama a karkashin killacewar gwamnati saboda adawar da yake yi da mahukuntan kasar.

A cikin bidiyon na Farideh Moradkhani ta ce: “Yanzu ne lokacin da dukkan kasashe masu ’yanci da dimokuradiyya za su janye wakilansu daga Iran a matsayin alama da kuma korar wakilan wannan gwamnati daga kasashensu.”

A ranar Alhamis din makon jiya da ce Hukumar Kare Hakkn dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta yanke shawarar kafa sabon ayarin masu bincike domin duba mumunan harin da jami’an tsaron Iran suka kai a kan masu zanga-zangar kin jinin gwamnati.

Sukar Jamhuriyar Musulunci ta Iran daga ’yan uwa na manyan jami’ai ba wani abu ne da ba a taba ganin irinsa ba.

A shekarar 2012, Faezeh Hashemi Rafsanjani, ’yar tsohon shugaban kasar, Akbar Hashemi Rafsanjani, an yanke mata hukumcin zaman gidan yari saboda “farfagandar kin jinin kasa.”

Hukumomin Iran sun bayar da belin dan fafutika kuma marubuci Hossein Ronaghi a ranar 26 ga Nuwamba don ya yi jinya, kamar yadda dan uwansa ya rubuta a shafin Twitter.

Damuwa na qa0ruwa game da lafiyar Ronaghi bayan da ya fara yajin kin cin abinci a watan Oktoba.