✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yar Ekweremadu na neman taimakon koda

Ta roki 'yan Najeriya su taimaka mata su ceto rayuwarta

Sonia Ekweremadu, ’yar tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ike Ekweremadu, ta roki ’yan Najeriya da su taimaka mata da kyautar koda.

Ta yi wannan roko ne yayin da mahaifanta suka shiga tsaka mai wuya a kokarinsu na ceto rayuwarta.

A shafinta na Instagram, Sonia ta roki al’umma da su taimaka wa rayuwarta da koda, sakamakon mawuyacin halin da take ciki.

“Shekaruna 25, kuma na kammala karatuna a fannin aikin jarida a jami’ar Coventry da ke Birtaniya.

“Ban iya ci gaba da karatun digiri na biyu da na faro a jami’ar Newcastle ba, sakamakon larurar kodar da na gamu da ita a shekarar 2019.

“Mahaifana sun yi iya kokarinsu wajen kai ni asibitoci daban-daban, amma abu ya ci tura.

“Yanzu haka ina Birtaniya ana min wankin koda na tsawon sa`o`i biyar sau 3zuwa 4 a sati guda.

“Wannan ya faru ne sakamakon rashin cika ka`idojin samun inshorar lafiya (NHS) ta kasar.

“Ba abu ne mai sauki ba, domin ga shi ya jefa iyayena a mawuyacin hali.

“Ba sai na cika ku da surutu ba, domin kowa ya san lamarin na gaban kotu yanzu haka.

“Sai dai ina fatan gaskiya za ta bayyana kan lamarin.

“Kafin wannan lokacin ina rokonku da ku dubi halin da nake ciki ku taimaka min.

“Sakamakon matsalata ta gado ce, ya sanya likitoci suka ce ba zai yiwu a sanya min ta dangi ba,” inji ta.

A karshe ta ce da zarar ta samu lafiya, za ta maida hankali wajen tallafawa masu irin larurarta.

Ekeremadu da mai dakinsa  dai sun yi yunkurin samo mata koda gun wani matashi, wanda ya kai su ga gurfana a gaban kuliya, sakamakon zargin safarar bil-Adama, da kokarin karbar sassan jikin mai karancin shekaru.

Daga baya dai kotun ta bada belin mai dakinsa Beatrice, yayin da ta cigaba da tsare shi har zuwa watan Oktoba, lokacin da za a fara zaman sauraren shari`ar.