✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yar haya ta sace yara kwana 3 da shigarta gida

Sun zo gidan ne ta hannun wani matashi da ke sana’ar tura kudi ta POS da dillanci a unguwar a ranar Lahadin makon jiya.

Al’ummar garin Suleja da ke Jihar Neja da ke fama da matsalar satar yara na tsawon lokaci kafin ya lafa a kwanakin baya, sun sake samun kansu a wannan matsala, inda a makon jiya aka sace musu yara biyu ta hanyar wani sabon salo.

Yaran biyu wa da kanwa, Abdullahi mai shekara 5 da Rahama mai shekara 3, an sace su ne a cikin gidansu da ke Unguwar Matar-Akawu a garin Suleja a ranar Larabar makon jiya, inda ake zargin wata sabuwar ’yar haya a gidan da aikata haka.

Mahaifin yaran, Malam Umar Abdullahi ya shaida wa Aminiya cewa matar mai kimanin shekara 25 ta kama hayar daki a gidan da suke haya ne tare da wani matashi mai kwatancin shekarunta a matsayin ma’aurata, kwana uku kafin aukuwar lamarin.

“Sun zo gidan ne ta hannun wani matashi da ke sana’ar tura kudi ta POS da dillanci a unguwar a ranar Lahadin makon jiya.

“Da farko wani matashi ne ya fara zuwa neman dakin hayar, amma sai mai gidan ya ce ba zai ba shi ba saboda yanayinsa yana dauke da gashi a murde da ake kira dada.

“Sai suka sake dawowa da wata da suka bayyana cewa ’yar uwarsu ce, ita ce ta shaida wa mai gidan cewa ba mai gashin ba ne zai zauna a dakin, wani daban ne da matarsa.

“Sun biya Naira dubu 30 kudin haya na shekara, da aka bukaci lambar wayarsu, sai suka ce a jira wadanda za su zauna a gidan su iso don ba da lambarsu,” in ji Malam Abdullahi.

Ya ce matasan sun bayyana kansu a matsayin masu sana’ar kida wajen taro (D.J), kuma ba a kai ga karbar lambar wayan wani daga cikinsu ba, har zuwa lokacin da lamarin ya faru.

Ya ce, “A ranar da lamarin ya faru iyalina ta gama dafa abincin rana sun ci tare da yaran, kafin karfe 2:00 na rana, sai ta shige cikin daki ta kwanta, ta bar yaran a falo suna wasa.

“Da misalin karfe 3:00 na rana bayan ta tashi, sai ta kula yaran ba sa nan, da aka bincika a kofar gida, sai aka sanar da ita cewa an ga sabuwar ’yar hayarta dauke da karamar yarinyar a kafada, babban kuma tana rike da shi a hannu suna tafiya.

“Wadanda suka gan su sun shaida mana cewa ba su yi tunanin komai a zuciyarsu ba.”

Ya ce a dan zaman kwana uku da suka yi a gidan, matar takan saya wa yaran gidan da na makwabta irin su biskit, kuma takan zauna da yaran makwabta a kofar gida tana ba su wayarta suna wasa da ita.

Ya ce kafin ficewar matar da yaran, namijin ne ya fara fita shi kadai, sannan da ta tashi fita ba ta rufe dakinsu ba.

“Bayan shiga dakin ne sai aka ga ba komai a ciki in ban da ledar daki da bokitin roba na wanka, inji shi.

Aminiya ta samu labarin cewa bayan shafe yammacin ranar ana neman yaran ba tare da nasara ba, an kai rahoton sace su ga ofishin ’yan sanda da dare, kafin a gayyaci mai gidan da wanda ya yi dillancin hayar a ranar Alhamis.

Majiyar ta ce mutanen biyu sun kwana a ofishin ’yan sanda, kafin a wuce da su zuwa hedikwatarsu da ke Minna a ranar Juma’ar da ta gabata, inda aka ba da belinsu washegari Asabar.

Kakakin ’Yan sandan Jihar, DSP Wasiu Abiodun wanda ya tabbatar da aukuwa lamarin, ya ce an ba da belin mutanen ne kan dalilai na rashin lafiya da nufin komawa ofishin bayan wani lokaci.

Sai dai wata majiya a unguwar ta ce an sake mutanen ne da nufin taimakawa wajen neman yaran da mutanen da ake zargi, da sharadin su koma a yau Juma’a.

Bayanai sun ce namijin ya bayyana kansa a matsayin dan asalin Jihar Edo, a yayin da macen ta ce ita ’yar kabilar Mada ce daga Jihar Nasarawa.

Lamarin ya ta da hankalin al’umma a garin na Suleja inda limamai ke ci gaba da jan hankalin al’umma su kara sa ido a kan yara da kuma masu shigowa unguwanni neman haya.