✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yar Najeriya ta haifi ’yan 6 bayan shekara 6 da haihuwar tagwaye

Wannan ya zo ne shekara shida bayan ta haifi tagwaye.

Wata ’yar Najeriya mai shekara 49 ta haifi jarirai ’yan shida, inda ta samu mata hudu da maza biyu. Wannan ya zo ne shekara shida bayan ta haifi tagwaye.

Kafar labarai ta BBC Pidgin ta ruwaito cewa, matar mai suna Doris Levi Wilson ’yar asalin Jihar Bayelsa ce, ta shafe shekara 21 da yin aure kafin ta haifi tagwaye namiji da mace shekara shida baya.

Doris da mijinta Mista Levi Wilson, sun yi aure ne a 1994 kuma tsawon shekaru suna kokari neman ciki, amma hakan bai samu ba. Sun yi ta ziyartar asibitoci daga wannan zuwa wancan a sassan kasar nan suna gwaji da magunguna iri-iri amma ba su samu nasara ba.

Daga karshe Doris ta koma neman magani a gida kuma ta yi imanin hakan ya taimaka mata wajen daukar cikin tagwayenta, Peremobowei Prince da Peremoboere Princess, a shekarar 2015.

Daga baya ta sha irin maganin da ta sha a baya lokacin da ta samu juna biyu ’yan shida wadanda aka sa wa suna; Miracle da Mercy da Merit da Marvis da Marvel da Mirabel.

Ta haife su ne a ranar 9 ga Fabrairun bana, kuma har zuwa ranar da ta haifi ’yan shidan ba ta san cewa, tana dauke da jarirai shida ba saboda ba ta yi hoton cikin ba.

Matan da ke wurin da suka yi mata tausa a matsayin wani bangare na kula ungozoma sun yi mamakin yadda suka karbi haihuwar jarirai masu yawa har shida a lokaci guda.

Mijin mai jegon ya taimaka matuka a yayin jinyar kuma ya yi farin ciki lokacin da aka fara jero masa jariran shida.

Ya fada wa manema labarai cewa, yana da matukar muhimmanci maza da mata su yi gwajin haihuwa saboda bambancin da ke tattare da haihuwa na iya nuna cewa, namiji ma yana bukatar magani.