✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yar Sanata Goje ta ajiye mukaminta bayan an kai masa hari a Gombe

Ana jiran ganin matakin da surukinsa da yaransa da ke Gwamnatin Inuwa Yahaya za su dauka.

Dokta Hussaina, ’yar tsohon Gwamnan Jihar Gombe, Sanata Danjuma Goje, ta ajiye mukaminta na Kwamishinar Muhalli da Gandun Daji a jihar.

Dokta Hussaina Danjuma Goje ta mika takardar ajiye aikin nata ne a yammacin ranar Asabar, matakin da ake gani na da nasaba da rikicin da yake faruwa tsakanin mahaifinta da Gwamna Inuwa Yahaya.

Ta yi murabus din ne washegarin harin da aka kai wa mahaifinta, inda wasu ’yan barandar siyasa suka hana shi shiga garin Gombe, wanda ya kai ga ba wa hamata iska tsakanin magoya bayansa da daya bangaren.

Ana zargin yaran Gwamna Inuwa Yahaya ne suka tare Sanata Goje da nufin hana shi shiga garin na Gombe a ranar Juma’a.

Bayan lafawar rikicin, an ga tsohuwar kwamishinar a saman bene tare da mahaifin nata a lokacin da yake yi wa magoya bayansa jawabi.

A takardar ajiye aikinta, tsohuwar kwamishinar ta gode wa Gwamna Inuwa da ya ba ta damar hidimta wa jihar a majalisar zartarwarsa, amma ta ce ta ajiye aikin ne saboda wani dalili na kashin kanta.

Wasu jama’ar gari dai na ganin matakin da ta dauka ya yi daidai domin ta nuna cewa ta san zafin mahaifinta, ta yi masa da’a kuma ta nuna cewa ita ’ya ce.

Yanzu masu lura da al’amura a jihar na jiran ganin ko shi ma surukin Sanata Danjuma Goje, wato Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu, Dasuki Jalo da sauran yaran Gojen da ke cikin gwamnatin Inuwa Yaha za su bi sahu.