✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yar Sardauna, Aisha ta rasu

Allah Ya yi wa ’yar Sardaunan Sakkwato, Alhaji Ahmadu Bello, mai suna Aisha rasuwa

Allah Ya yi wa ’yar Sardaunan Sakkwato, Alhaji Ahmadu Bello, mai suna Aisha rasuwa.

Hajiya Aisha Ahmadu Bello ta rasu tana da shekara 76, a wani asibiti a birnin Dubai na Haddaddiyar Daular Larabawa, bayan fama da rashin lafiya, kamar yadda danta, Hassan Dambaba, ya sanar.

Marigayiyar, wadda aka fi sani da suna Hajiya A’i ita ce ta biyu a cikin ’ya’yan marigayi Sardauna, kuma mata  ce ga marigayi Marafan Sakkwato, Alhaji Ahmad Danbaba.

Ta rasu ta bar ’ya’ya biyar, cikinsu har da Magajin Garin Sakkwato, Hassan Danbaba da Asma’u, matar Sarkin Sudan, Shehu Malami.

A halin yanzu an fara shirye-shiryen dawo da gawarta Najeriya don yi mata jana’iza.