✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yar shekara 10 mai rubutu da kafa na son zama likita

Mahaifinta ya saki uwar, ya tafi ya bar su saboda ta haifi 'ya mai lalura

Wata ’yar shekara goma, wadda hannuwanta ba sa aiki, ta bayyana burinta na zama likita da kuam yadda take amfani da kafarta wajen yin rubutu da sauran abubuwa.

Fatima Kabiru wadda ke zaune a Dogarawa, Karamar Hukumar Sabon Gari ta Jihar Kaduna, ta ce, duk da lalurar da take da ita, “Duk wani abu da mai hannu ke yi ni ma da kafa nake yi.

“Ina yi wa kaina wanka da shafa hoda, sa kwali, kuma ta bagarancin abinci duk da kafa nake yi, haka ma sai dai abin da ba zai gagara ba, haka rubutu da dai sauransu duk da kafa nake yi.”

Ta ci gaba da shaida wa Aminiya cewa, “Kuma ba na samun wata tsangwama daga kawayena ko kuma wadanda nake mu’amala da su.

“Burina a rayuwa shi ne, duk da cewa hannayena ba su yin aiki, amma ina son zama likita ni ma, domin in rika  kula da marasa lafiya,” a cewarta.

Yadda aka haife ta

Mahaifiyarta, Amina Idris, ta bayyana cewa daga farkon samun cikin ’yar tata mai lalura har zuwa yadda ta haifeta.

Kamar yadda ta ce, “Ita ce ’yata ta biyar a jerin haihuwata kuma daga kanta ban sake haihuwa ba saboda mijina ya sake ni sakamakon cewa ya gaji da dawainiyar Fatima.

“Cikin bai wahalar da ni ba kamar sauran na ’yan uwanta, wajen haihuwa ne da nakuda kawai na dan fuskanci matsala, don haka sai a asibiti na haihu, ba kamar na sauran ’yan uwanta ba.

“Domin kamar za a yi mun aiki sai ma’aikatan suka yi ta yin yadda sai da suka ciro ta, ba tare da an yi aiki ba.

“To bayyan sun ciro ‘yar daga cikina sai suka fahimci cewa hannayenta duk sun karereye domin kusan da karfi suka ciro ta.

“Daga nan sai aka shiga boye mun, ba a so na sani domin kada nace ban yarda ba, bayan hakan ya faru sai muka fara kokarin cewa ta sami lafiya amma, ina tunda Allah haka Ya so Ya gan ta.

Mijina ya sake ni saboda na haifi ’ya da lalura

“A kan kokarin muga ta sami lafiya ne mahaifin ya ce shi ya gaji, ba zai iya ba, don haka ya sake ni, ya tafi ya bar ni a gidansu, tunda dama muna gidan gado ne tare da ’yan uwansa.

“To daga nan sai ’yan uwan suka ce su ba su yarda in tafi ko’ina ba, sai daga baya ne na dawo gidanmu domin mu ci gaba da rayuwa tare da yarana su biyar da ya bar ni da su,” a cewarta.

Ta ce, “Haka na kama sana’ar saye da sayarwa shi kuma babban dan nawa yana sana’a, idan ya dawo makaranta, haka muke ta rayuwa.

“Faitma yarinya ce mai kwazo kuma, don haka ko wanka ba ta so a yi mata, wani lokaci idan na ce zan cuda ta ba ta so, haka take yi, duk kusan abin da kasa ni, ita da kanta take yi wa kanta.

“Kuma ba mu taba zuwa neman taimakon kowa ba sai daga makarantarsu ne suka yi kokarin sanar da shugaban karamar hukuma, wanda yanzu ya shigo cikin lamarinmu, sai kuma yazu da Allah Ya kawo ku,” in ji ta.