✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yar shekara 4 ta mutu a rijiya a Kano

An tsamo yarinyar a sume, kafin daga bisani ta ce ga garinku nan.

Wata yarinya ’yar kimanin shekaru hudu a duniya ta rasu a Jihar Kano sakamakom fadawa rijiya da ta yi.

Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Alhaji Saminu Abdullahi ya fitar ranar Talata a birnin na Dabo.

A cewarsa, lamarin ya auku ne ranar Litinin a Unguwar Kofar Waika kusa da Masallacin Karmawi da ke Karamar Hukumar Gwale ta jihar.

“Mun samu kiran gaggawa da karfe 2:05 na ranar Litinin daga wani mai suna Alkasim Ibrahim kan afkuwar lamarin, kuma take muka tashi tawagar ceton hukumar kuma sun isa gurin da karfe 2:20,” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa “an tsamo yarinyar a sume, kafin daga bisani ta ce ga garinku nan.”

Kazalika Abdullahi ya ce hukumar tuni ta mika gawar yarinyar ga iyayenta ta hannun mai unguwar Kofar Waika, Isma’ila Yusuf, domin yi mata jana’iza.