✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yar shekara biyu ta kamu da coronavirus

Wata yarinya ’yar shekara biyu ta kamu da cutar coronavirus a Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Abeokuta bayan fitowar sakamakon gwajin cutar da aka…

Wata yarinya ’yar shekara biyu ta kamu da cutar coronavirus a Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Abeokuta bayan fitowar sakamakon gwajin cutar da aka yi mata.

Kamuwar ’yar yarinyar ta haifar da taron gaggawa inda hukumar asibitin ta umarci duk wadanda da suka yi mu’amala da ita da su mika kansu domin a yi musu gwajin cutar.

“Gaskiya ne har an killace ta ana kula da ita kuma da alama maganin na karbar ta.

“Ana feshin magani da dakin da aka kwantar da ita an kuma fara aikin gano wadanda ta yi mu’amala da su”, inji kakakin asibitin Segun Orisajo.

Wata likitar kananan yara a asibitin, Dokta Chinyere Uzodinma ta ce an rufe dakin karbar marasa lafiya masu bukatar kulawar gaggwa har sai an tantance matsayin lafiyar wadanda ke ciki.