✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yara 10 sun mutu sakamakon shan gurbataccen magani a Yemen

An fara gudanar da bincike domin gano tushen maganin da kuma yadda aka yi ya shiga kasar.

Rahotanni daga Sanaa, babban birnin kasr Yemen, wasu kananan yara 10, masu fama da cutar sankarar bargo sun riga mu gidan gaskiya bayan da suka sha wani gurbataccen magani da aka yi fasakwaurinsa zuwa kasar.

Hukumomin lafiya na kasar sun ce, yanzu haka akwai wasu yara tara a kwance cikin mawuyacin hali sakamakon amfani da maganin.

A cewar hukumomin Yemen, an fara gudanar da bincike domin gano tushen maganin da kuma yadda aka yi ya shiga kasar.

Bayanai sun nuna abu ne mai sauki samun magungunan da aka yi fasakwaurinsu a asibitocin kasar.

Matsalar da ake danganta ta da rashin kudi da kuma wadatattun kayan aiki a asibitocin kasar.

Kusan rabin kayayyakin asibitocin kasar a lalalce suke tun bayan barkewar yakin basasa a kasar.