✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yara 33,000 za su ci gajiyar karatu daga gida a Katsina

Akalla yara ‘yan makaranta 33,000 ne za su ci gajiyar shirin karatu daga gida a Jihar Katsina. Wani shirin bunkasa ilimi mai suna ULS ne…

Akalla yara ‘yan makaranta 33,000 ne za su ci gajiyar shirin karatu daga gida a Jihar Katsina.

Wani shirin bunkasa ilimi mai suna ULS ne ya bullo da tsarin karatu daga gidan ga dalibai a jihar.

Shirin, wanda ya samu tallafi daga Hukumar Kula da Ilimin Bai Daya ta jihar ta Katsina da kuma wani asusun tallafa wa ilimi na kasa da kasa an bullo da shi ne domin daliban su ci gaba da karatu daga gida saboda zaman gidan da annobar COVID-19 ta tilasta.

Daraktan ULS a Arewacin Najeriya, Umar Farouk Bello ne ya bayyana hakan yayin wani taron horas da jami’an da za su koyar da daliban.

Ya ce shirin ya zabo mutum daya daga kananan hukumomi guda biyar daga kowacce mazabar dan Majalisar Dattijai, inda mutane 15 ke nan za su samu horon yayin da kowanne daga cikinsu zai horas da mutum 10 a karamar hukumarsa.

Darektan ya ce jami’an da za su samu horo kuma su ne za su wayar da kan yaran da kuma iyayensu a kan shirin karatun.

Kowanne daga cikinsu kuma zai zakulo iyalai 20 dauke da yara goma-goma da zai kula da su domin tabbatar da bayar da tazara a tsakaninsu.

Umar Farouk ya ce za a rika watsa shirye-shiryen ne a gidajen rediyo da talbijin na jihar ta Katsina da kuma kafafen sada zumunta irinsu ga iyayen da suke da sukunin mallakar manyan wayoyi.

Kazalika za a gudanar da gwaji ga daliban kafin da kuma bayan shirin wanda zai shafe tsawon makonni shida yana gudana.