✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yaran da aka yi garkuwa da su a Neja sun shaki iskar ’yanci

Mutanen sun kubuta bayan an biya ’yan bindiga kudin fansa.

Wasu mutum biyar da ’yan bindiga suka sace, ciki har da wasu yara biyu ’yan gida daya a Anguwar Kwankwashe da ke Karamar Hukumar Suleja ta Jihar Neja, sun shaki iskar ’yanci.

A makon jiya Aminiya ta karo rahoton yadda ’yan bindigar suka kai hari a garin, inda suka balla wasu gidaje da wani otal, sannan suka yi awon ga da mutane.

  1. Barcelona ta maka PSG a kotu don dakile kulla yarjejeniya da Messi
  2. Gwamnonin PDP za su yi taro kan makomar Shugaban Jam’iyyar

Amma biyu daga cikin wadanda abin ya rutsa da su sun tsere daga hannun masu garkuwar a lokacin da suka kai su cikin daji.

Wani dan uwan wadanda aka sace, wanda ya bukaci a boye sunansa, ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho cewa an sako su ne a ranar Litinin da misalin karfe 6:23 na safe bayan an biya kudin fansa, amma bai bayyana ko nawa ne ba.

Ya ce wanda ya kai wa ’yan bindigar kudin fansar ya kira su a waya a lokacin da ya kai kudin wani waje da ba su sani be, tare da ’yan bangar da za su karbe su.

“Duk wadanda aka sace, ciki har da yara biyu a Anguwar Kwankwashe a makon da ya gabata an sake su ranar Talata, bayan an biya kudin fansa, amma ba zan iya bayyana nawa ba ne saboda sha’anin tsaro,” inji shi.

Wani hafsan dan sanda a garin Madalla, CSP Adamu Mohammed, ya tabbatar da kubutar wadanda aka sacen, amma bai bayyana nawa aka biya kudin fansa ba.