✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yari da Marafa sun sauya sheka daga APC zuwa PDP

A bara ce ikon jami'iyyar APC a Jihar Zamfara ya subuce daga hannun Yari da Marafa.

Tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari da Sanata Kabiru Garba Marafa sun sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP.

Shugaban jam’iyyar adawa ta PDP a jihar, Kanal Bala Mande mai ritaya ne ya sanar da hakan jim kadan bayan an kammala wani taron masu ruwa da tsaki a Gusau, babbar birnin jihar a ranar Lahadi, 17 ga watan Afrilu.

Mande ya bayyana wannan na zuwa ne bayan zaman yanke shawara da suka gudanar a kan batun sauya shekar Yari da Marafa, inda suka cimma yarjejeniyar aiki kafada da kafada don ciyar da jam’iyyar gaba.

“Duk mun aminta za mu yi aiki don ci gaban jam’iyyar sannan PDP a jihar ta yi maraba da su a cikinta.

“Za mu tabbatar da gaskiya da adalci ga dukkan mambobinmu har bayan mun lashe zabe a 2023.

“Za a sanar da ranar gagarumin bikin dawowarsu jam’iyyamu daga bisani amma za mu aiwatar da dukkan yarjejeniyar da muka cimma a yayin taron masu ruwa da tsaki.”

Mai magana da yawun tsohon gwamna Yari, Alhaji Ibrahim Muhammad Birnin Magaji ne ya tabbatar wa Aminiya hakan sai dai bai yi wani karin bayani ba.

“Eh gaskiya, za mu sauya sheka zuwa jam’iyyar adawa ta PDP, kuma wannan shi ne kadai abin da zan iya fada a yanzu haka,” a cewar Birnin Magaji.

A shekarar da ta gabata ce ikon jam’iyyar APC a Jihar Zamfara ya subuce daga hannun Yari da Marafa bayan gwamna Bello Matawalle ya koma koma jam’iyyar.