✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sanata Yarima ya yi alhinin mutuwar tsohon Jakadan Najeriya a Amurka

Tsohon gwamnan Jihr Zamfara, Sanata Ahmed Sani Yarima, ya bayyana alhaninsa game da rasuwar tsohon Jakadan Najeriya a kasar Amurka, Mai shari’a Sylvanus Adiewere Nsofor.…

Tsohon gwamnan Jihr Zamfara, Sanata Ahmed Sani Yarima, ya bayyana alhaninsa game da rasuwar tsohon Jakadan Najeriya a kasar Amurka, Mai shari’a Sylvanus Adiewere Nsofor.

Mai kula da Kungiyoyi magoya bayan Yarima a kudu maso gabashin kasar, Farfesa Orikeze Vitalis Ajumbe ne ya bayyana sakon ta’aziyyar a madadin tsohon gwamnan a ranar Asabar.

Yarima, ya bayyana rasuwar Mai shari’a Nsofor a matsayin babban rashi ga Najeriya, duba da irin gudunmawar da ya bayar wurin kyautata alaka da dangartaka tsakanin Najeriya da kasar Amurka lokacin yana jakadanci a Amurka.

Ya ce mai shari’a Nsofor mutum ne mai gaskiya da nagarta, bisa la’akari da rawar da ya taka a kasar nan.

“Marigayi Mai shari’a Nsofor mutum ne mai kyawawan dabi’u wanda tauraruwarsa ta yi haske a tsarin harkokin shari’a a Najeriya.

“Muna jajantawa gwamnatin tarayyar Najeriya da Jama’ar Jihar Imo, bisa rasuwar mai shari’a Sylvanus Nsofor.

“Muna kuma yi wa iyalin marigayi Nsofor addu’ar samun juriya da hakurin rashi,” in ji shi.