✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yariman Zazzau ya taya Bamalli murnar zama sabon sarki

Yariman Zazzau, Alhaji Munir Jafaru ya taya sabon sarki Ahmed Nuhu Bamalli murna

Daya daga cikin na gaba-gaba wajen neman kujerar Sarkin Zazzau kuma Yariman masarautar, Alhaji Munir Jafaru ya taya sabon sarki, Ahmed Nuhu Bamalli murna.

Yarima a sanarwa da ya fitar ranar Laraba ya ce ya amince da nadin Bamallin a matsayin sabon sarki ya kuma bayyana nadin nasa a matsayin nufin Allah tar da addu’ar Allah Ya yi wa sabon sarkin jagora, Ya kawo zaman lafiya da cigaba a tsawon lokacin da zai shafe a kan karaga.

“Ya zama wajibi mu karbi nadin a matsayin nufin Allah mu kuma taya sabon sarkin murna, Allah Ya yi masa jagora.

“A madadin ni kaina da iyalaina da abokai da magoya baya da masu fatan alheri, ina mika cikakkiyar godiyata gare ku saboda jajircewarku da fatan alheri.

“Na yi matukar murna,” inji Yariman na Zazzau.

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya amince da nadin Ambasada Ahmed Nuhu Bamallin a matsayin Sarkin Zazzau na 19 bayan rasuwar Alhaji Sehu Idris a kwanakin baya.