✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yarinyar da aka haifa ranar da aka haifi iyayenta

Ba kasafai ndai ake samun irin haka ba a duniya

Wasu iyalai a birnin Alabama na kasar Amurka sun kasance uba da uwa da ’ya da suka hada ranar haihuwa, lamarin da ba cika samu ba.

Iyayen masu suna Cassidy da Dylan Scott sun haifi ’yarsu ta farko ce a ranar 18 ga Disamban nan, ranar da ta kasance ranar haihuwar su biyun, kamar yadda shafin Facebook na Asibitin Mata da Yara na Huntsville Hospital for Women & Children ya bayyana.

“Wannan lokaci ne na farin ciki ga kowane iyali, amma an samu karin farin ciki ga wannan iyali, saboda su ukun sun hada ranar haihuwa,” Asibitin na Huntsville ya rubuta a shafinsa na Facebook.

Ya kara da cewa: “Wannan gaskiya ce. A ranar Lahadi 18 ga Disamba, damar samun haihuwa daya a cikin haihuwa 133,000 ta auku, lokacin da aka haifi ’yarsu Lennon. Ba ta iso duniya ba, sai da misalin karfe 12:30 na dare, a daidai lokacin da uwa da uban suka fara nasu bikin ranar haihuwar. Mu hadu mu taya wannan iyali murnar wannan haihuwa.”

An yada wannan labari na shafin asibitin na Facebook sau 1,700 cikin awanni kadan da sanarwar, inda mutum 250 suka yi sharhi a kai.

Masu amfani da shafin Facebook sun taya iyalan Scott murna inda daya daga cikinsu ya rubuta: “Abin jin dadi! Wannan abu ne mai faranta rai. Muna taya ku murna. Kuma barka da ranar haihuwarku dukkanku.