✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yarinyar da aka yanke wa al’aura ta warke

Ana zargin matsafa ne suka yaudare ta zuwa cikin wani kango suka yanke mata al'aura.

Karamar yarinyar nan da a wasu matsafa suka yanke wa al’aura a Jihar Bauchi ta warke.

An sallami Hawa’u, mai shekara shida daga asibitin bayan wata hudu da faruwar al’amarin, ta kuma koma hannun iyayenta a Karamar Hukuamr Jama’are ta Jihar.

A watan Disamban 2020, Aminiya ta kawo rahoton zargin yadda wasu matasa biyu a unguwar Gandu da ke garin Jama’are suka yaudari karamar yarinyar suka kai ta cikin wani kango inda suka yanke mata al’aura domin su yi tsafi da shi.

Daga baya Gwamnatin Jihar Bauchi ta dauki nauyin jinyar yarinyar a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano (AKTH) da ke Kano.

Bayan sallamar ta, Kwamishinan Lafiya na Jihar, Dokta Aliyu Mohammed Maigoro da mahaifanta sun gabatar da ita ga Gwamnan Jihar, Bala Mohammed, wanda ya ba umarnin daukar nauyin jinyar.

Kwamishinan ya yi kira ga al’umma da su tashi tsaye wurin yakar “irin wannan dabbancin”, domin gwamnati kadai ba za ta iya ba.

Ya kuma shawarci iyayen yarinyar da su tabbata ba sa barin ta ita kadai a duk lokacin da za su aike ta ko tura ta zuwa makaranta.