✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yarjejeniyar zaman lafiya: Ba a ga Tinubu ba a wajen rattaba hannun ’yan takara

A ranar Alhamis, ‘yan takarar Shugaban Kasa daga jam’iyyu daban-daban a zaben 2023 mai zuwa suka hadu a Abuja don rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman…

A ranar Alhamis, ‘yan takarar Shugaban Kasa daga jam’iyyu daban-daban a zaben 2023 mai zuwa suka hadu a Abuja don rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya.

Sai dai kuma wani abu da ya dauki hankalin jama’a game da haduwar ‘yan takarar, shi ne rashin ganin dan takarar jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Tinubu a tsakanin takwarorinsa.

Sai dai an ga Mataimakinsa a takarar, Sanata Kashim Shettima, wanda ya tsaya a madadinsa.

‘Yan takarar da aka gani wajen sun hada da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da Peter Obi na jam’iyyar LP da kuma Rabi’u Musa Kwankwaso na jam’iyyar NNPP.

Kwamitin Zaman Lafiya na Kasa (NPC) karkashin jagorancin tsohon Shugaban Kasar Najeriya, Abdulsalami Abubakar ne ya jagoranci rattaba hannu kan yarjejeniyar.

Ga karin hotuna daga zaman: