✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yaro mafi kiba a duniya ya rage nauyi da kilo 107

Yaron da ya fi kowane yaro kiba a duniya mai suna Arya Permana ya rasa rabin kibarsa bayan ya daure cikinsa da wata roba da…

Yaron da ya fi kowane yaro kiba a duniya mai suna Arya Permana ya rasa rabin kibarsa bayan ya daure cikinsa da wata roba da ta taimaka masa wajen dame ciki kuma ya rika cin abinci marasa maiko tare da yawaita motsa jiki.

Arya wanda yanzu ke da shekara 14, ya yi kokarin rage nauyinsa da kimanin giram dubu 107.955 ta hanyar sauya yanyin rayuwarsa.

Ya taba kai nauyin giram dubu196.859 (sama da kilo 196) a lokacin da yake shekara 11 kamar yadda ya yi wa wata kafar labarai karin haske.

A lokacin da yake shekara 9 nauyin Arya ya kai giram dubu 127 .006. Arya na zama ne a kauyen Jaba ta Yamma (West Jaba)da ke kasar Indonesiya, kuma yana yin wanka a kwamin ruwa (swimming pool).

Kibarsa ta sa mafi yawan kayan da yake sanyawa sun yi masa kadan, hakan ya sa yake daura mayafi saboda yawan cin kayan makulashe ciki har da abincin gwangwani, kuma abincin da ya fi sha’awa shi ne taliya.

Ayra yana sha’awar sha da cin abinci mai kara kuzari, inda yake cin abinci mai yawa a kullum, kuma abincinsa shi kadai zai iya ciyar da matasa biyu.

Mahaifiyar Ayra mai suna Rokayah mai shekara 39 da mijinta Ade Somatri mai shekara 50 kuma manomi, sun nuna matukar damuwa game da lafiyar dansu, hakan ya sa suka tilasta masa sauya abincinsa.

A shekara uku da suka wuce bayan ya sanya robar da take rage masa teba ya fara sauya abincin da ya saba ci, sannan ya fara motsa jiki, Ayra ya kashe kudi kusan Fam 231 (kimanin Naira dubu 122 da 81) kamar yadda kafar labarai ta The Sun ta ruwaito.

Ayra yana iya tafiya ’yar kadan ce a baya, amma yanzu yana iya tafiya mai nisan kilomita 3 a rana, kuma yana wasan kwallon Kwando da wasan babura da wasu wasannin motsa jiki.

Ya dawo yana iya zuwa makaranta. Ayra ya ce: “A shekarar 2015, ban taba tsammanin zan iya rage kiba haka ba. Yanzu ina jin dadin jikina, akwai bambanci da baya.”