✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yaron da iyayensa suka daure a cikin dabbobi ya samu lafiya

Bayan samun saukinsa gwamnati za ta ci gaba da kula da lafiyarsa bayan gina masa gida tare da iyayensa

Gwamnatin Jihar Kebbi ta inganta lafiyar Jibril Aliyu, yaron da aka gano iyayensa sun daure shi a cikin dabbobi na tsawon lokaci abin da ya haifar masa da cutar kwakwalwa har yake cin kashinsa da na dabbobin.

A watan Agustan bara aka samu labarin yaron mai shekara 12 a Unguwar Badariya da ke Birnin Kebbi, inda Kungiyar Lauyoyi Mata da wasu na sa-kai suka shiga lamarin.

Gwamnati ta shiga lamarin, inda ta mika yaron ga Shugaban Asibitin Tunawa da Sarki Yahaya da ke Birnin Kebbi, Dokta Yahaya Aliyu Bunza tare da mataimakansa 20 domin ceto rayuwar yaron.

Yaron an gano shi ne a ranar 9/08/2020 aka mika shi ga ma’aikatan kiwon lafiya ranar 10/08/2020 sannan suka dawo da shi ranar Talata 7/12/2021, ke nan ya yi wata 15.

Daya daga cikin ’ya’yan kungiyoyin da suka taimaki yaron kafin gwamnati ta shiga lamarin, ta bayyana wa wakilimnu cewa, “Ba zan ce komai ba kan lamarin yaron domin an hana mu yi magana.”

Mai bai wa Gwamnan Kebbi Shawara kan Harkokin yada labarai, Yahaya Sarki, ya ce bayan samun saukin yaron gwamnati ta dauki matakan ci gaba da kula da lafiyarsa bayan gina masa gida shi da iyayensa da kuma ba shi tallafin karatu.