✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yau ake bikin bai wa Sarkin Kano sandar mulki

A ranar Asabar za a bai wa Alhaji Aminu Ado Bayero sandar mulkin Masarautar Kano.

A ranar Asabar 3 ga watan Yuli, 2021 za a mika wa Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero sandar mulkin Masarautar Kano.

Za a gudanar da kasaitaccen taron ne a filin wasa na Sani Abacha da ke Birnin Kano, inda aka tanadi kujeru na kimanin manyan baki na alfarma da sauran mahalarta kimanin 20,000.

“Baki da dama za su halarci bikin ciki har da Mataimakin Shugaban Kasa da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa,” kamar yadda Fadar Sarkin Kano ta sanar.

Fadar Sarkin Kano ta ce za a girke jami’an tsaro 4,000 da suka hada da DSS, sojoji, jami’an Civil Defense da sauran jami’an tsaro, domin tabbatar da aminci da cikakken tsaro har a kammala bikin.

Da yake bayani, Dan-Dalan Kano, Abbas Dalhatu, ya kara da cewa an ware kujeru 3,000 ga manyan baki, da wasu kujeru 13,000 na sauran mahalarta kasaitaccen bikin.

Bayan kammala mika wa Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayeor sandar mulki, za a gudanar da hawa na musamman, daga baya kuma Sarki zai zaga a cikin gari don gaisawa da jama’arsa.

Dalhatu, ya bayyana cewa an nada marigayi Alhaji Ado Bayero sarautar Kano a Filin Wasa na Sani Abacha shekara 53 da suka gabata, kuma wannan karon ma za a nada magajin nasa a filin wasan.

Aminu Bayero ya zama Sarkin Kano na 15 daga tsatson Gidan Sarautar Fulani na Masarautar Kano a ranar 9 ga watan Maris, 2020 bayan Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya sauke Sarki Muhammadu Sanusi II.

Dalhatu, ya ce, “A ranar Litinin, Sarki zai zaga cikin gari a kan dokinsa don gaisawa da jama’a.

“Zagayen zai fara daga Fadar Sarki zuwa unguwar Fagge, Sabon Gari daga nan kuma ya sake dawowa fada.”

Tun da farko Madakin Kano, Alhaji Nabahani Ibrahim, ya shaida wa Aminiya cewa za a shafe kwanaki biyar cur ana bikin mika sandar ga Sarki Aminu.

Alhaji Nabahani, ya ce bikin da aka fara tun a ranar Alhamis, 1 zuwa Litinin 5 ga watan Yuli zai fara ne da wata lacca sannan a kammala shi da hawa.

“Tsohon Shugaban Jami’ar Karatu daga Gida ta Kasa (NOUN), Farfesa Abdallah Uba Adamu ne zai gabatar da laccar mai taken ‘Masarautar Kano a Jiya, Yau da Gobe’, a dandalin bikin yaye dalibai ta Jami’ar Bayero da ke Kano”.