✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yau ake fara hako danyen mai a Arewa Maso Gabashin Najeriya

Kimanin shekara biyu ke nan da dakatar da makamancinsa da aka fara a Jihar Borno, sakamakon matsalar rashin tsaro.

A yau ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da aikin hakar danyen mai na farko a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Fara hakar danyen man a Rijiyar Mai ta Kolmani 809 da 810 da ke jihohin Bauchi da Gombe na zuwa ne kimanin shekaru shida bayan gano wasu rijiyoyin mai a Arewacin Najeriya a 2016.

Nasarar hako man zai sanya jihohin Bauchi da Gombe a jerin masu arzikin mai a Najeriya, wanda ke nufin za su shiga sahun jihohin da ake ware wa kaso 13 cikin 100 na kudaden shigar Gwamnatin Tarayya daga bangaren danyen mai.

Bugu da kari, za su samu karin kudaden haraji daga kamfanonin da za su rika aikin hakar man da jigilarsa da dangoginsu; ga kuma samar da karin ayyukan yi.

Kimanin shekara biyu ke nan da dakatar da makamancinsa da aka fara a Jihar Borno, sakamakon matsalar rashin tsaro.

Arzikin man Najeriya

Kamfanin mai na NNPC ya gano arzikin mai da yawansa ya kai na kasuwanci a Arewacin Najeriya ne a jihohin Kogi da Neja a yakin Arewa ta Tsakiya sai kuma Borno, Bauchi da kuma Gombe a yankin Arewa maso Gabas.

Tun daga lokacin da aka fara hako danyen mai a Najeriya ya zama babban abin da gwamnatin 2ta dogara da shi wajen samun kudaden shiga.

Kamfanin NNPC ya yi hasashen arzikin man da ke karkashin kasa a Najeriya ya haura lita biliyan 50.

Tuni dai kasar Jamhuriyyar Nijar, makwabciyar Najeriya ta Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma, ta gano mai a yankin ta kuma fara hako shi.

Hakan ya kara wa Najeriya kwarin gwiwa a hasashenta na samun mai a yankin.

Alfanon arzikin mai

Danyen mai shi ne makamashin da aka fi amfani da shi a duniya, don haka yake zaman babbar hanyar kudaden shigar gwamnatocin kasashe.

A Najeriya, Gwamnatin Tarayya kan ware wa jihohi masu arzikin mai kashi 13 cikin 100 na kudaden da aka samu daga bangaren mai.

Illar arzikin mai

Sai dai kuma yankunan da ake hakar man sukan yi fama da matsalolin gurbacewar muhalli sakamakon ayyukan hakar man.

A kan haka ne aka yi ta samun yawaitar korafe-korafe a yankin Neja Delta da aka fara samun mai.

Zargin kamfanonin hakar mai da lalata musu muhalli ba tare da biyan su wata diyya ba ya haifar da matsalar tsaro inda wasu bata-gari kan fasa bututun danyen mai domin su sace.

Hakan yana jawo wa kasar asarar makudan kudade na man da ake tsiyayewa da wanda ake sacewa, baya ga kudin da take kashewa wajen gyaran bututan man da kuma gadinsa.

Akwai kuma matsalar masu satar man da ake zargin suna hadin gwiwa da jami’an tsaro.

A ko a baya-bayan nan sai da aka gano wani budutun satar danyen mai daga Bututun Escravos a kusa da wani sansanin soji a yankin Neja Delta.

Kamfanin NNPC ya ce Najeriya na yin asarar danyen mai kusan lita miliyan uku a duk wata, sakamakon ayyukan bata-garin.

Shin an dauki darasi?

Haka ne ma ya sa ake ganin ya kamata Gwamnatin Tarayya ta dauki matakan da suka dace a yankin Arewa maso Gabas da aka gano rijiyoyin danyen mai domin hana aukuwar irin matsalolin da aka samu a yankuna masu arzikin mai a Kudu.

Matattun matatan mai

A yayin da Najeriya ke gano arzikin mai a karkashin kasarta da kuma hako shi, har yanzu kasar ta dogara ne da tataccen mai da ake shigo mata ta da shi ne daga kasashen waje.

A baya-bayan nan kuma ana fama da matsalar karancin mai baya ga tashin gwauron zabo da ya yi a gidajen mai a sassan kasar.

Gwamnatocin kasar sun shafe shekaru suna kokarin farfado da matatun mai guda hudu da kasar ke da su a Kaduna, Fatakwal, da Warri, amma har yanzu bukata ba ta biya ba.

Hasali ma, ’yan kasar na ganin asarar ake yi wajen gyaran matatun, a tsawon shekaru.

Hakan ne ma ya sa wasu ’yan kasar ke da ra’ayin a cefanar da matatun.

A halin yanzu dai gwamnatin Najeriya na sa ran ganin matatar mai da attajirin Afirka dan kasar, Aikin Dangote ke ginawana kasar.

Gwamnatin Najeriya ta zuba jari a matatar, wadda ita ce mafi girma a Nahiyar Afirka.

A watan Oktoba gwamantin ta ba da aikin gyaran Matatar Mai ta Kaduna (KRPC) ga kamfanin Daewoo na kasar Koriya ta Kudu.

Kamfanin ne kuma aka bai wa aikin gyaran Matatar Mai ta Warri, tun da farko.

Makomar danyen mai

A halin yanzu kasashen Turai na kokarin ganin an daina amfani da shi zuwa wasu shekaru a nan gaba, a koma amfani da makamashin tsirrai da kuma hasken rana.

Ana yin wannan gangami ne da zummar takaita sauyin yanayi da ake dangantawa da hayakin da injina ke fitarwa.

Hakan na nufin nan gaba farin jini da kasuwar danyen man za su ragu a kasuwar duniya, wanda kuma zai kawo nakasu ga kudaden shigar gwamnatocin da suka dogara da shi.