✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yau ake rufe yakin neman zaben shugaban kasa

Dokar zaben Najeriya ta haramta duk wani nau'in yakin neman zabe awa 24 kafin ranar zabe

Daga karfe 12 na daren yau Alhamis 23 ga Fabrairu, 2023, za a fure yakin neman zaben ’yan takarar shugaban kasa da Majalisun Tarayya da za a gudanar ranar Asabar.

Dokar Zaben Najeriya ta haramta yin duk wani nau’in yakin neman zabe ko tallata dan takara daga sa’a 24 kafin ranar zabe.

A yayin rubuta wannan rahoton, kusan awa 12 ya rage wa daukacin jam’iyyu da ’yan takara su yi duk abin da za su iya, su kuma rufe yakin neman zabensu, sannan a fafata a akwatunan zabe a ranar Asabar.

Jam’iyyu 18 ne ke zawarcin kujerar shugaban kasa bayan kammala wa’adin Shugaba Muhammadu Buhari na biyu a ranar 29 ga watan Mayu.

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa za a gudanar da zabukan ne a mazabu 1,491 da ke kananan hukumomi 774 da ke jimillar rumufunan zabe 176, 846.

’Yan Najeriya ne za su yi alkalanci a zaben mai mutum miliyan 95.5 da suka yanki katin zabe, wadanda akasarinsu matasa ne, masu shekara 18 zuwa 35, ko da yake kawo yanzu babu alkaluman adadin wadanda suka karbi katin zabensu.

Manyan jam’iyyu

Jam’iyyar APC mai mulki kasar tun 2015 na neman ci gaba da jan ragamar kasar na karin shekara hudu, a yayin da babbar jam’iyyar adawa ta PDP wadda ta mulki kasar na tsawon shekara 16, bayan dawowar tsarin dimokuradiyya daga 1999 zuwa 2015 na neman sake dawowa.

Bugu da kari, zaben na bana ya zo da sabon abu, inda ake da wasu kananan jam’iyyu biyu, LP da kuma NNPP da suke tashe da kuma samun magoya baya a wannan karon.

A yayin da APC da PDP suka tsayar da dattawan da suka haura shekara 70, LP da NNPP na bugun kirji da kasancewar ’yan takararsu masu jini a jika da suka bar kyakkyawan tarihi a mukaman da suka rike a baya.

Batun shekarun ’yan takara dai ya dade yana tayar da kura a zabukan Najeriya, inda gabanin zaben 2019 Gwamnatin Tarayya ta yi dokar rage yawan shekarun tsayawa takara domin a dama da matasan kasa.

Manayan ’yan takara

APC ta tsayar da tsohon Gwamnan Jihar Legas (1999-2007) kuma Uban Jam’iyyar na kasa, Asiwaju Bol Ahmed Tinubu, a yayin da PDP ta tsayar da Fsohon Mataimkin Shugaban Kasa Atiku Abubakar (1999-2007).

Karo na shida ke nan Atiku yake neman zama shugaban kasa a yayin da Tinubu ke tutiyar cewa shi ya fi kowa dacewa ya mulki kasar a wannan karon bayan Buhari.

Dan takarar LP, Peter Obi, shi ne tsohon Gwamnan Jihar Anambra, kuma tsohon abokin takarar Atiku a lokacin zaben 2019 da Buhari ya lashe.

A nasa bangaren, yana takama da matasa, kasancewarsa mai karancin shekaru a cikin manyan ’yan takara.

Hakazalika, dan takarar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yana takama da kasancewa mai jini a jika yana kuma bugun gaba da irin ayyukan da ya yi a lokacin da yake Gwamnan Jihar Kano, ministan tsaro.

Yana kuma takama da farin jininsa, inda a 2015 ya zama na biyu a zaben dan takarar shugaban kasa na APC, wanda Buhari ya lashe.

Muhimman batutuwa

Zaben na zuwa ne a yayin da Najeriya ke tsaka da fama da matsalar tattalin arziki bayan Gwamnatin APC ta yi sauyin takardun Naira 200, N500 da kuma N1,000.

Sauran abubuwan da ke ci wa kasar tuwo a kwarya sun hada da sha’anin tsaro, tsadar man fetur da rashin ingantattun ababen more rayuwa da suka hada da bangaren ilimi, lafiya, sufuri, da kuma uwa uba makamshi da wutar lantarki.