✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yau ce ranar fara yakin neman zaben 2023 a Najeriya

’Yan takara 18 za su fafata a zaben shugaban kasa na 2023 wanda masu zabe miliyan 84 za su kada kuri'a

A yayin da aka fara yakin neman zaben 2023 a Najeriya, ’yan takara 18 ne za su fafata domin samun kaso mafi tsoka daga kuri’un masu zabe miliyan 84 a kasar.

Manyan ’yan takarar sun hada da tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na Jam’iyar NNPP, da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar na PDP, tsohon Gwamnan Anambra, Peter Obi na LP, da kuma tsohon Gwamnan Legsa, Bola Tinubu na APC.

Akwai wasu sauran ’yan takara 14 daga jam’iyyu daban-daban.

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce ’yan Najeriya 84,004,084 ne suka yi rajistar kada kuri’a, daga bayanan da ta tattaro a watan Agusta.

Buga kugen yakin neman zaben zai sanya ’yan takara 18 tallata kawunansu a tsakanin kwanaki 147.

INEC din ta sanya 25 ga watan Fabrairun 2023, a matsayin ranar zaben kujerun Shugban Kasa da na ’yan majlisun tarayya.

’Yan takara da magoya bayansu, hadi da jam’iyyun baki daya sun shirya jerin abubuwa daban-daban da za su aiwatar, domin fara yakin neman zaben.

APC

Daraktan yada labaran APC, Bayo Onanuga, cikin wata sanarwa, ya bayyana dage yakin neman zaben jam’iyar da za a fara ranar Laraba da addu’o’i na musamman da kuma tattaki.

Babban Daraktan Yakin Neman Zaben Tinubun ya ce an yi hakan ne domin kara cakuda jiga-jigai a kwamitin yakin neman zaben jam‘iyyar.

PDP

PDP za ta fara nata yakin neman zaben ne da kaddamar da littattafai guda uku da dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar zai yi, domin tallata kansa ga ’yan Najeriya.

Daga nan ne zai kaddamar da kwamitin yakin neman zabensa, da kuma fara ayyukansa a hukumance, duk da rikicin da jam’iyar ke fama da shi na cikin gida.

Rikicin dai ya kara bayyana karara bayan da Gwamnan Abia, Okezie Ikpeazu da sauran jagororin jam’iyyar suka kaurace wa taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki na shiyyoyoin siyasa shida na Najeriya, da Atikun ya kira.

Sai dai ana zargin kusancin Ikpeazu da Gwamnan Ribas, Nyesom Wike ne ya sanya ya ki halartar taron da aka gudanar a Jihar Inugu.

A makon da ya gabata Wike da sauran makusantansa suka fice daga majalisar yakin neman zaben Atikun, bisa hujjar kin sauka daga kujerar shugaban jam’iyyar ta su da Iyorchia Ayu ya yi.

NNPP

Sakataren yada labaran NNPP na kasa, Dokta Agbo Major, ya bayyana wa wakilinmu ta wayar tarho cewa, jam’iyar za ta fara yakin neman zabenta ne daga Arewa ta Tsakiya a mako mai kamawa.

LP

Ita ma Jam‘iyar LP ta ce za ta tattauna da masu ruwa da tsakinta, domin fitar da tsare-tsaren da za ta yi amfani da su a yakin neman zaben.

 

Daga: Rahima Shehu Dokaji Kano, da Ismail Mudashir, da Baba Martins, da Terkula Igidi, da Saawua Terzungwe (Abuja), da Abiodun Alade (Lagos),da Linus Effiong (Umuahia),