✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yau ce ranar iyaye maza ta duniya

Ranar Lahadi ta mako na uku a kowane watan Yuni ce aka kebe domin tunawa da iyaye maza ta duniya, kuma a bana (2020) ranar…

Ranar Lahadi ta mako na uku a kowane watan Yuni ce aka kebe domin tunawa da iyaye maza ta duniya, kuma a bana (2020) ranar ta yi dai-dai da 21 ga watan Yuni.

An fara bikin tunawa da iyaye maza ne a shekarar 1910 a yankin Spokane a gundumar Washington ta kasar Amurka.

Wata da ake kira Sonora Smart Dodd ce ta fara bikin ranar tunawa da iyaye mazan a ranar 19 ga watan Juni, 1910  domin tunawa da mahaifinta dan mazan jiya da ya yi yakin duniya, William Jackson Smart.

Zuwa yanzu jama’a da dama a fadin duniya na tunawa da wannan rana inda suke jinjina irin gudunmawar da iyayensu maza suka ba su a rayuwarsu.

A Najeriya mutane da dama na tuna wa da wannan rana a kafafen sadarwa na internet inda suke sanya hotunan iyayensu maza suna masu yi masu addu’a da godiya ko jinjina bisa gudunmawar da suka yi masu a rayuwa.

Ko da me kuke tunawa da iyayenku maza? Me kuke yi don nuna godiyarku a gare su?