Yau take Ranar Matasa ta duniya | Aminiya

Yau take Ranar Matasa ta duniya

    Isiyaku Muhammed

A yau Laraba 11 ga watan Agusta ce Ranar Matasa ta duniya na 2020.

An kirkiri ranar ce domin jajantawa da tunawa da tashin-tashinan Soweto, wato Suweto Uprising wanda ya wakana a ranar 16 ga watan Yuni na shekarar 1976.

A lokacin an kase dubban matasan dalibai bakaken fata a yayin rikicin wariyar launin fata (apartheid) a sa’ilin da suke gudanar da zanga-zangar lumana daga makarantarsu zuwa Filin Wasan Orlando, inda jami’an tsaro suka yi musu kwantar bauna, suka halaka su.

Don haka ne matasa a kasar Afirka ta Kudu suka fara amfani da ranar domin nuna gudunmuwar matasa wajen kwato ’yancin mutanen kasar daga mulkin nuna wariyar launin fata.

Taken ranar na bana shi ne “Amfani da matasa wajen daukan matakai a duniya”.

Ranar ta bana za ta taimaka wajen nuna yadda matasa tun daga matakan unguwanni da kasashe za su shiga a dama da su wajen daukar matakan ciyar da duniya gaba.

A shekarar 1999 ce Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana ranar 12 ga Agusta a matsayin Ranar Matasa ta Duniya, duk da cewa har yanzu wasu kasashe sun bambanta ranakun da suke gudanar da bikin ranar.

Har yanzu Najeriya ba ta ware ranar matasan ba, amma daidaikun kungiyoyin matasa a Najeriya suna gudanar da bikin ranar.

Daga cikin wadanda suka taya matasa murnar ranar, akwai tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar.

A sakon da ya aike ta kafar Mediun, Atiku ya ce yana taya matasa a duk fadin duniya murnar wannan rana.

Ya ce saboda sanin muhimmancin matasa ya sa ya yi alkawarin ba matasa kashi 40 cikin dari a gwamnatinsa a lokacin da yake fafutikar zaben 2019.

A daya bangaren kuma, Shugaban Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila da Gwamnan Jihar Imo Sanata Hope Uzodimma sun tattauna kai tsaye da matasa a wani taro da Majalisar Matasa ta Najeriya ta shirya.

Sauran wadanda za su yi magana a taron sun hada Ministan Wasanni, Sunday Dare da Ministan Harkokin Mata, Pauline Tallen da tsohon Gwamnan Bauchi, Muhammad Abubakar da dan wasan barkwanci, Mr Macaroni, wanda ake yi wa lakabi da Freaky-Freaky.