✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yaushe Buratai ya tare a Arewa Maso Gabas?

Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai, ya tare a yankin Arewa Maso Gabas don sa ido a kan yadda yaki…

Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai, ya tare a yankin Arewa Maso Gabas don sa ido a kan yadda yaki da Boko Haram ke tafiya. 

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ambato Rundunar Sojin Kasa Kanar Sagir Musa, wanda ya bayyana haka, yana cewa daga can ne kuma Janar Buratai zai sa ido a kan ayyukan sauran dakarunsa a fadin Najeriya.

Sai dai kuma Kaanar Musa bai bayyana takamaimai lokacin da Babban Hafsan na Sojin Kasa ya tare a yankin ba.

Idan ba a manta ba, tun a shekarar 2015 bayan rantsar da shi a zangon mulkinsa na farko, Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci manyan hafsoshin rundunonin soji na Najeriya su koma yankin na Arewa Maso Gabas don a yi ta ta kare a yakin da ake yi da Boko Haram.

Kuma a watan Yunin shekarar ta 2015 kakakin Rundunar Sojin Kasa na wancan lokacin, Kanar (kamar yadda yake a lokacin) Sani Usman Kukasheka, ya fitar da sanarwa cewa har ma an shirya cibiya inda hafsoshin rundunar za su yi aiki.

“Daga yanzu, daga wannan cibiya za a rika sa ido da jagorantar yaki da ta’addanci da ta da kayar baya”, a cewar Kukasheka a wata sanarwa da ya fitar a Maiduguri.

Kanar Sagir Musa dai ya ce Janar Buratai ne ya sanar da tarewarsa a yankin lokacin da yake jawabi ga dakarun Sansanin Soji na Musamman da ke Ngamdu a jihar Borno.

Ya kara da cewa Babban Hafsan na kai ziyarar aiki ga dakarun da ke fagen daga tun daga ranar 4 ga watan Afrilu.

“Yayin kewayen, ya ziyarci Sansanin Soji na 1 da ke Mulai da kuma Babban Sansanin Zaratan Soji na 12 da ke Chabbol kusa da Maiduguri ranar 8 ga watan Afrilu inda ya gana da jami’an soji ya kuma yi jawabi ga dakaru.

“Bugu da kari, Babban Hafsan na Sojin Kasa ya ziyarci Sansanin Bakin Daga da ke Alau Dam, sannan da kanshi ya jagoranci dakaru suka fita sintiri a Dazukan Mairimari da Maigilari”, inji Kanar Musa.

Wannan lamari dai na zuwa ne a daidai lokacin da sojojin Chadi, wadanda aka ce Shugaba Idris Deby da kansa ne ya jagorance su, suka kaddamar da hare-haren kakkabe mayakan Boko Haram daga yankunan kasarsu,

‘Yan Najeriya da dama za su yi fatan jin cewa sojojin kasar sun yi nasarar kakkabe masu ta da kayar bayan dungurungum, kamar yadda ake cewa na Chadi sun yi, sakamakon wannan mataki da Janar Buratai ya dauka.

Masu suka dai sun yi ta kira ga Shugaba Buhari ya sauke manyan hafsoshin sojin kasar ganin cewa lokacin ritayar su ya yi kuma rikicin Boko Haram ya ki ci ya ki cinyewa, ga kuma kalubalen masu garkuwa da mutane da mahara a sassan kasar daban-daban.

Shin ko a wannan lokaci Buratai zai yi gwanintar da za ta rufe bakin masu sukar?