✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yaushe ’yan Arewa za su hankalta?

Shin laifin me yankin Arewa ya yi wa wani?

A wannan makon, GIZAGO (08065576011) ya yi tsokaci ne game da al’amuran da suka shafi Arewa da al’ummarta.

Arewacin Najeriya duk da irin albarkatun da Allah Ya hore mata na yawan jama’a da noma da kiwo da fadin filin kasa, amma yankin Kudu ya yi mata fintikau wajen ci gaba a fannonin rayuwa.

A batu na gaskiya, al’ummar Arewa tana bukatar saiti kuma wannan saitin ba wai ga talakawa ba kadai.

Al’umma tun daga kan shugabanni da ma’aikata da malaman addini da ’yan kasuwa – kowa da kowa na bukatar saiti, domin kuwa al’amuran yankin Arewa a baibai suke tafiya.

A yankin Arewa, mun yi sakaci, sakacin da ya sanya a kullum sai ci baya muke yi, duk da cewa mu ne muka gaji kyawawan al’adu da dabi’u tun daga dauri.

Mu ke da madaukakin addini, addinin da ya shahara wajen saita rayuwar al’umma zuwa nagarta. Mun watsar da duk wani shisshike mai nagarta, mun rungumi akasin nagarta, mun kama kaskanci.

Ga duk al’ummar da ke son ci gaba, mai son sama wa kanta daraja da kima, mai son lafiya da zaman lafiya da yalwar arziki, harkar ilimi take runguma kuma ta ba shi matukar muhimmanci.

A Arewa, al’amarin ba haka yake ba, domin kuwa tunda dadewa aka juya wa ilimi baya, aka rungumi kishiyarsa. Mun bar yaranmu maza da mata babu wani tallafi da jagoranci ta bangaren ilimi.

Mun bar yaranmu suna bin kwararo da tituna, suna barace-barace. Matasanmu kuwa, tuni aka saki hannuwansu, babu abin da suke na kirki, daga bangar siyasa, sai shaye-shayen kayan maye.

Mun samu tabarbarewar dabi’a, inda ayyukan assha suka yawaita.

A yau ba sai gobe ba, kullum sai ka ji labarin cewa an yi wa karamar yarinya fyade. Mace-macen aure ya zama ruwan dare. Yankunanmu sun zama dandamalin zubar da jini da fashi da makami da garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

Har yaushe muka kai ga wannan lalacewa haka? Shin laifin wane ne, sakacin wane ne ya jefa mu cikin wannan mummunan yanayi?

Shin laifin shugabanni ne ko na malaman addini ko na iyaye?

Allah Ya hore wa Arewa faffadar kuma yalwatacciyar kasar noma amma abin takaici mun jefar.

Gwamnatocinmu suna gani abinci na neman fin karfinmu, babu wani kwakkwaran ingantaccen shirin tallafa wa harkar noma domin ciyar da al’umma abinci da samar da ayyukan yi ta hanyarsa.

Matasanmu majiya karfi sai kaura suke yi daga yankunanmu zuwa Kudu, inda suke gudanar da kaskantattun sana’o’i.

Ba karamin kaskanci ba ne ga dan Arewa ya bar yankinsa a matsayin ’yantacce, ya tafi Kudu yana aikin gadi da yankan farce da tura baro da wankin takalma da nufin neman dukiya, alhali ga babbar dukiya nan ta noma ya bari a yankinsa.

Shin ta yaya aka yi kishiyoyinmu a kullum suke kokarin ganin sun inganta al’amuran rayuwarsu, mu kuwa ba mu da wani tanadi na kirki?

Mutanen Kudu a kullum suna jajircewa suna inganta harkokinsu na ilimi, kasuwanci, sana’a da ma noma. Hatta ga batun siyasa, tsarinsu na musamman ne – suna tafiya da murya daya domin kwato hakkokin yankinsu daga Gwamnatin Tarayya.

Me ya sa Arewa ta zama sansanin yaki da kashe-kashe? Me ya sa Arewa ta zama sansanin barace-barace? Me ya sa Arewa ta zama sansanin shaye-shayen kayan maye? Me ya sa Arewa ta zama koma-baya ta fuskar ilimi da masana’antu da kere-kere?

Muna ji muna gani aka kakaba mana dasisar kashe-kashen al’umma, inda aka rika yi wa shugabanninmu da attajiranmu da malamanmu dauki-dai-dai.

Shin mun manta yadda aka kakaba mana Boko Haram, aka kakaba mana fadan makiyaya da manoma? Ko kuwa mun mance yadda aka dasa mana gabar kabilanci da bambanci addini da bangaranci?

Shin mun mance yadda yankin Arewa a can baya ya zama yankin zaman lafiya da aminci? Mun mance yadda a can baya muke zaune tsakaninmu da juna cikin salama da ’yan uwantaka? Shin mun mance yadda aka yi wa sarakunanmu na gargajiya barazana?

Muna nan aka yi wa Sarkin Gwoza kwanton bauna, aka yi masa kisan gilla. Muna nan a can baya, aka dubi sarki mafi daraja da muhibba a Arewa, Sarkin Kano, marigayi Ado Bayero, aka kai masa farmaki da nufin halaka shi, ya sha da kyar.

Haka aka yi ta wulakanta sarakuna a yankunan Borno da Adamawa da Yobe. Shin me ya sa muka amince da wannan kaskanci?

Malaman addininmu masu daraja ba su tsira ba. Shin mun mance yadda ’yan ta’adda suka dauki rayuwar muzakkarin malami, Sheikh Ja’afar Mahmud Adam?

Mun mance yadda aka halaka Shaikh Auwal Albani Zariya da Ustaz Dan Maishiyya a Sakkwato? Ko kuwa mun mance yadda aka kai wa Shaikh Dahiru Bauchi farmaki a Kaduna?

Shin ta yaya yankin Arewa ya yi sakaci, ya bari rayukan dattijai mazan jiya suka salwanta? Ko mun mance da yadda aka yi wa marigayi Janar Mamman Shuwa kisan gilla a gidansa?

Mun mance yadda da rana tsaka, ranar Jumu’a mai daraja, aka kai harin bam a Babban Masallacin Juma’a na garin Kano, inda aka halaka mutane sama da dari biyu, aka jikkata wasu da dama?

Mun mance yadda aka yi ta tsorata mu a kasuwanni da wuraren ibada? Mun mance yadda duk aka kirkiri shingaye a manyan titunanmu, ana ci mana zarafi, ana wulakanta mu?

Shin laifin me yankin Arewa ya yi wa wani? Shin wani ya tsine mana ne ko kuwa ya la’ance mu da har muka zura idanuwa ana yi mana abin da aka ga dama?

Shin mun zama talasurai ne da ba za mu mike tsaye mu sama wa kanmu daraja da muhibba ba?

Lallai lokaci ya yi da ya kamata sarakunanmu da shugabanninmu na siyasa da shugabanninmu na addini (Musulmi da Kirista) da manyan ma’aikatanmu na gwamnati da manyan ’yan kasuwarmu su hadu a bagire daya, su yi nazari da basirar da Allah Ya ba su, su tattauna hanyoyin tallafa wa yankin nan na Arewa, domin ceto shi daga balbalcewa.

Muna bukatar tsari da saiti a harkar ilimi. Muna bukatar tsari da saiti a fannin noma da kasuwanci. Muna bukatar saiti a bangaren siyasa da mulki.

Muna bukatar kyakkyawan tsarin gudanarwa a fannin adddini da yadda muke gudanar da shi.

Babu shakka wannan ne lokacin da ya kamata mu taru mu yi wa junanmu saiti, mu yi karatunta-natsu, mu dauki hanyar gyara domin ceto kanmu da al’iummarmu da yankinmu na Arewa daga ci gaba da susucewa.

Allah Ya taimake mu, amin!