✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yawaita yin azumi zai iya haifar da ciwon koda – Shugabar NAFDAC

Shugabar Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Maguguna (NAFDAC), Farfesa Mojisola Adeyeye ta ce yawaita yin azumi ba kakkautawa na iya jawo larurar koda. Adedeye…

Shugabar Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Maguguna (NAFDAC), Farfesa Mojisola Adeyeye ta ce yawaita yin azumi ba kakkautawa na iya jawo larurar koda.

Adedeye ta bayyana hakan ne ranar Litinin a ganawarta da manema labarai a Abuja.

Ta kuma ce amfani da abinci ko magunguna marasa inganci na iya haifar da lalcewar koda da mutuwa baki daya.

A cewarta, “Kasarmu cike take da mabiya manyan addinan nan biyu, wato Musulinci da Kiristanci. Kuma dukkansu na azumi sosai.

“Amma ya kamat mu sani dole ne sai jiki ya samu daidaito da wadataccen ruwa a jiki kafin ya yi aiki yadda ya kamata.

“Wasu sai su shafe kwanaki 20-30 suna azumi kuma ba su sha ruwa ba ko kadan, wanda haka ne ke lalata koda.

“Shan ruwa wadatacce shi ne ke taimaka wa kodar dan Adam wajen tacewa da sirka ruwan jikin dan Adam don jiki gaba daya yayi aikin da ake bukata.

“Don haka masu yawan yin azumi su yi shi da lura, kar su yi abin da zai taba lafiyar kodarsu”, in ji ta.

A karshe ta gargadi al’umma kan amfani da magungunan da masu talla a titi ke sayarwa da masu kafa shaguna a layi ba tare da sun yi rajista ba.

A nasa bangaren, Shugaban Kungiyar Likitocin Koda ta Kasa, Dokta Adanze Asinobi, cewa ya yi kimanin mutane miliyan 869 ne a duniya ke fama da larurar, kuma mafi yawansu a Najeriya suke.