✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yawan al’ummar duniya zai kai biliyan 8 a makon gobe —MDD

Al’ummar duniya za ta ci gaba da karuwa zuwa biliyan 8 da rabi a shekarar 2030.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa yawan al’ummar duniya zai karu zuwa biliyan 8 a tsakiyar watan Nuwamban nan da muke ciki.

MDD ta ce adadin zai ci gaba da karuwa a hankali a cikin gomman shekaru masu zuwa.

Hukumar Kula da Yawan Jama’a ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa al’ummar duniya za su kai biliyan 8 a ranar 15 ga watan Nuwamba.

Ta yi kiyasin cewa karuwar za ta kasance ninki 3 kenan na yawan al’ummar duniya a shekarar 1950, lokacin da ake da mutane biliyan 2 da rabi.

Jami’ar hukumar, Rachel Snow ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa cewa bayan karuwar da al’ummar duniya suka yi cikin sauri a cikin shekarun 1960, yanzu yana tafiyar hawainiya.

Yadda al’ummar duniya ke yaduwa ya ragu daga kashi 2 da digo 1 a tsakanin shekarun 1962 da 1965 zuwa kasa da kashi 1 a shekarar 2020.

Adadin na iya raguwa zuwa kasa da rabin kashi zuwa shekarar 2050, sakamakon yadda ake ci baya wajen samun rabo na haihuwa, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniyar ta yi hasashe.

Sai dai majalisar ta yi wani hasashen na daban da ke nuni da cewa duba da yadda ake samun karin tsawon rai, inda ake kai wa shekaru 72, da kuma karuwar wadanda suka kai munzulin haihuwa, al’ummar duniya za ta ci gaba da karuwa zuwa biliyan 8 da rabi a shekarar 2030.

Haka kuma, ta yi hasashen al’ummar za su kai biliyan 9 da dubu dari 7 a 2050, sannan a 2080 adadin zai kai biliyan 10 da dubu dari 4.