✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yawan dauke wuta: Lauya na neman kamfanin lantarki ya biya shi diyyar N200m

An shigar da karar ne a gaban Babbar Kotun Jihar Neja da ke zamanta a Suleja.

Wani lauya mai zaman kansa, Musa Abdullahi, ya maka Kamfanin Rarraba Hasken Lantarki na Shiyyar Abuja (AEDC) a gaban kotu, yana neman ya biya shi diyyar Naira miliyan 200 saboda yawan dauke wuta.

Lauyan, wanda ya shigar da karar mai lamba NSHC/SD/27/2022, ya kuma roki kotun da ta ba kamfanin umarnin biyan diyyar cikin wata shida saboda yadda ya ce ana yawan dauke musu wutar ba gaira ba dalili.

Kamfanin Dillancin Labarai Na Najeriya (NAN) ya rawaito cewas an shigar da karar ne ranar hudu ga watan Maris, a gaban Mai Shari’a Mariya Isma’il ta Babbar Kotun Jihar Neja da ke zamanta a garin Suleja.

Musa Abdullahi dai na karar kamfanin na AEDC ne a madadin al’ummomin yankunan Dawaki, Mata Akawu, Suleja Club, Maje, Kwamba, Bakasi, Gangare Kwata, Chaza, Fadar Sarki, Hassan Dallatu, Church Road, Rafin Sanyi, Paolosa da kuma Kwankwashe; dukkansu a Karamar Hukumar Suleja ta Jihar Neja.

Lauyan dai na so ne kotun ta fayyace masa ko kamfanin na bin dokokin Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) da kuma Kundin Samar da Wutar Lantarki na Najeriya na shekarar 2005.

A cewar mai karar, yawan dauke wutar ya yi matukar kassara kanana da matsakaitan sana’o’i, tare da tilasta wa gine-gine da dama su koma wa amfani da injinan janareta.

Ya ce injinan na da matukar illa ga lafiya da muhalli, baya ga tilasta wa masu sana’o’i da yawa rasa abin yi.

Sai dai ya yi korafin cewa duk da yanayin da ake ciki, wasu yankunan kamar na APC Quarters da titin Kaduna Road da PDP Quarters da ke garin na Suleja na samun wutar ta kusan sa’a 24.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton dai, kotun ba ta kai ga sa ranar fara sauraron ba. (NAN)