Yawan haihuwar ’ya’ya ya hana mu samun ci gaba — Gwamnatin Nijar | Aminiya

Yawan haihuwar ’ya’ya ya hana mu samun ci gaba — Gwamnatin Nijar

Shugaban Nijar, Mohamed Bazoum
Shugaban Nijar, Mohamed Bazoum

Gwamnatin Nijar ta bayyana cewa yawan haihuwar ’ya’ya barkatai shi ne babban musababbin da ke janyo wa kasar koma-baya da hana ta samun ci gaba.

Wannan dai na zuwa ne yayin da a halin yanzu ake gudanar da wani taron kwanaki biyu domin tattaunawa kan yadda za a rage yawan haihuwa a kasar.

Taron wanda aka kaddamar a ranar Talata, Shugaba Mohamed Bazoum ke jagorantarsa, ya jaddada matsayin gwamnatinsa na ganin mata sun rage haihuwa barkatai a kasar.

A jawabinsa, Bazoum ya ce wannan taro, ina da kyakkyawan fatan cewa zai taimaka wa mata wajen daidaita rayuwarsu tare da amfanin ’ya’yan da za su haifa da kuma makomarsu.

“Kamar yadda na taba fada a can baya, matukar muna haihuwar ’ya’ya barkatai, to lallai za mu gaza daukar dawainiyar ilmantar da su, idan har muka gaza ilmantar da su kuwa, to a nasu bangaren za su haifi ’ya’yan da za su kasance dalilin gaza habbaka tattalin arziki balantana samar wa kanmu ci gaba.”

Alkaluma sun tabbatar da cewa matukar ’ya’ya mata suka samu ilimi na akalla karamar sakandare, to ko shakka babu su ne za su fi taimakawa wajen samar da ci gaba a cewar shugaban na Nijar.

“A game da batun ilmantar da ’yan mata da kuma tabbatar da cewa sun kammala karamar sakandare, wannan ya sa gwamnati da taimakon abokan huldarta za ta gina makarantu da kuma daukar dawainiyyar ilimin ‘yaya mata, muna fatan yin hakan ba tare da bata lokaci ba” inji Shugaba Bazoum.

Rahotanni sun ce Sarakunan gargajiya da malaman addini daga sassan kasar na halartar taron wanda ake tattaunawa kan batutuwan tsarin iyali da kare hakkin ’yan mata.

Shugaba Bazoum ya kuma shawarci sarakuna da su kuduri aniyar ganin cewa daga yanzu ba wanda zai sake aurar yarinyar da ba ta kosa ba, ta yadda talakawa za su yi koyi da su a kan wannan batu na kare yara kanana daga matsalolin da ke tattare da auren dole da auren wuri.

Muryar Amurka ta ruwaito cewa, babban makasudun wannan taro da ake kira Symposium des Chefs traditionnels yana nazari a kan matsalolin da ke mayar da hannun agogo baya wajen ganar da al’ummar kasar muhimmancin ilimantar da ’ya’ya mata da kuma tsarin iyali bayan shafe shekaru ana yi wa wannan batu na kayyade iyali mummunar fahimta.