✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yawan masu Coronavirus a duniya ya haura miliyan 1

Yawan mutanen da suka kamu da cutar coronavirus a duniya daga bullarta sama da wata uku da suka wuce zuwa yanzu ya haura miliyan daya.…

Yawan mutanen da suka kamu da cutar coronavirus a duniya daga bullarta sama da wata uku da suka wuce zuwa yanzu ya haura miliyan daya.

Wata kididdiga da Jami’ar Johns Hopkins ta Amurka ke wallafawa ta nuna cewa a daren jiya adadin ya tsallake makin kidaya ya shiga lissafin miliyan daya da ‘yan kai a kasashe ko yankuna 181.

Alkaluman dai sun nuna cewa, daga cikin wannan adadi, kusan mutum 53,000 ne suka mutu yayin da wasu kusan 210,000 suka warke.

Kididdigar ta kuma nuna cewa kusan rubu’in mutanen da suka kamu da cutar a Amurka suke, yayinda kusan rabi ke nahiyar Turai.

Bugu da kari alkaluman sun nuna cewa galibin wadanda suka rasu sakamakon kamuwa da cutar, kusan mutum 14,000, a Italiya suke.

Adadin wadanda suka kamu da cutar dai ya yi tashin gwauron zabi ne a wata guda da ya wuce: tun daga lokacin da aka fara kididdigar a watan Janairu har zuwa ranar 13 ga watan Maris ba a samu adadin wadanda suka kamu ya kai 10,000 a yini ba in ban da ranar 13 ga watan Fabrairu, lokacin da aka samu sama da 15,000.

Amma tun daga nan ba a samu kasa da 10,000 a yini ba, adadin kuma ya yi ta hauhawa sosai har sai da ta kai a ranar 2 ga watan Afrilu kadai an samu mutum fiye da 80,000.

Sai dai ana ganin hakikanin yawan wadanda suka kamu da cutar ya haura abin da alkaluman na Jami’ar Johns Hopkins ke nunawa.

Kasashen Afirka da ke kan gaba a yawan wadanda suka kamu zuwa lokacin hada wannan rahoton su ne Afirka ta Kudu mai mutane 1,462, da Aljeriya mai mutane 986, da Masar mai 865, da Morocco mai 708, da kuma Tunisiya mai 455.

Wasu daga cikin kasashen Afirka ta Yamma da ke da wadanda suka kamu su ne Burkina Faso mai mutane 288, da Ghana mai 204, da Senegal mai 195, da Ivory Coast mai 194, da kuma Jamhuriyar Nijar mai 98.

Alkaluma na baya-bayan nan da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta fitar, wadanda ke cikin lissafin Jami’ar Johns Hopkins din, sun nuna cewa an tabbatar da mutane 184 na dauke da cutar a Najeriya.