✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yawan Musulmi ya karu a Birtaniya da Wales

Kididdigar yawan al’ummar Birtaniya da Wales ta nuna adadin Musulmi na karuwa, yayin da adadin Kiristoci ya gaza rabin jama’ar yankunan biyu

Kididdigar yawan al’ummar Ingila da Wales ta nuna cewa, adadin Musulmi na karuwa, yayin da adadin Kiristoci ya gaza rabin jama’ar yankunan biyu, kuma a karon farko ke nan da ake samun haka.

kididdigar wadda aka saba fitar da ita duk bayan shekara 10, ta nuna yadda yawan Musulmi ke havaka, amma dai babu addinin da ke da mabiya masu yawa kamar addinin Kiristanci.

Mutum miliyan 27.5 ko kuma kashi 46.2 cikin 100 sun gabatar da kansu a matsayin Kiristoci a Ingila da Wales a kididdigar 2021, lamarin da ke nuna cewa, adadinsu ya ragu da kashi 13.1, idan aka kwatanta da kididdigar shekarar 2011.

Yawan Musulmi kuma ya kai miliyan 3.9 ko kuma kashi 6.5 cikin 100, lamarin da ke nuna cewa, adadin Musulmin ya karu daga kashi 4.9 a kididdigar 2011.

Mabiya addinin Hindu ne ke matsayi na uku wajen yawan mabiya a Birtaniya da Wales, inda suke da yawan da ya kai miliyan 1. (rfi)