✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yawan Mutanen Najeriya yanzu ya kai miliyan 206 – NPC

Hukumar Kidaya ta Kasa NPC ta ce a yanzu kiyasi ya nuna yawan al’ummar Najeriya ya kai kimanin miliyan dari biyu da shida. Shugaban Hukumar…

Hukumar Kidaya ta Kasa NPC ta ce a yanzu kiyasi ya nuna yawan al’ummar Najeriya ya kai kimanin miliyan dari biyu da shida.

Shugaban Hukumar na Kasa, Nasir Kwarra ne ya sanar da hakan ranar Talata a birnin Abuja yayin wani taron manema labarai dangane da ci gaba da aikin shata kan iyakoki wanda ake kira Enumeration Area Demarcation domin kidayar al’ummar kasar rankatakaf.

Wannan na zuwa ne bayan shekaru biyu da Hukumar NPC ta kiyasta cewa yawan al’ummar kasar ya kai miliyan dari da casa’in da takwas.

Kwarra ya ce tun bayan da Najeriya ta gudanar da kidatyar al’umma shekaru 14 da suka gabata, a yanzu zai wuya a iya gano hakikanin adadin al’ummar kasar.

Ya ce: “Idan ba a gudanar da kidaya ta hakika ba a hukumace, abin da kawai za mu iya shi ne hasashe kuma hakan ya sanya muka kiyasta cewa zuwa shekarar 2020, yawan mutanen Najeriya zai kai miliyan 206.”

Alhaji Kwarra ya ce, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne kadai yake da ikon sanar da lokacin da za a gudanar da kidayar al’ummar Najeriya ta gaba.

Sai dai Alhaji Kwarra ya ce ya yi amanna Shugaban Kasar zai yi abin da ya dace na ba da dade wa ba.

Yayin karin haske dangane da aikin shata kan iyakoki da tantance kananan hukumomin kasar, Kwarra ya ce tuni aka kammala da kananan hukumomin 260 cikin 774 da ke fadin tarayyar kasar.

Aminiya ta fahimci cewa gwamnatin ta tsara aikin shata tantance iyakokin ne domin a samu saukin gudanar da kidayar a duk lokacin da aka tashi.

Ya bayyana cewa mataki na 11 na aikin zai fara a ranar 9 ga watan Disamban 2020, kuma ya kare a ranar 20 ga watan Janairun 2021.