✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a Najeriya yanzu ya kai miliyan 18 – UNICEF

Asusun Tallafa wa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF), ya ce akalla yara miliyan 18.5 ne ba sa zuwa makaranta a Najeriya. UNICEF ta…

Asusun Tallafa wa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF), ya ce akalla yara miliyan 18.5 ne ba sa zuwa makaranta a Najeriya.

UNICEF ta ce adadin ya haura a bana idan aka kwatan da shekarar 2021, da aka samu miliyan 10.5.

Shugaban Hukumar Kula da Ilimin Makiyaya ta Kasa (NCNE) Farfesa Bashir H. Usman, ne ya bayana hakan a wani taron kara wa juna sani, da aka shiryawa mambobin kwamitocin Gudanarwa na Makarantu (SBMC), da kuma Kungiyar Iyaye mata (MA), domin yaki da rashin zuwa makaranatar yara a yankin Arewa maso yammacin Najeriya da aka gudanar a KAduna.

Acewarsa UNICEF fiye da kaso 60 na wanna adadi mata ne, yayin da miliyan 3.5 kuma suka fito daga tsatson makiyaya.

“A shekarar 2022, UNICEf ta bada rahoton yara miliyan 18.5 da ba sa zuwa makaranta.

“Wannan adadin ya zarta na shekara 2021, wanda ya kara jefa yankin Afirka da shi ne yankin da ya fi kowanne yawan yaran da ba sa zuwa makaranta cikin garari a duniya.

“A Najeriya, abin ya fi kamari a yankin arewa maso yamma, musmaman jihohi irinsu Jigawa, da Kaduna, Da Katsina, da Sokotyo.

“Jihohi irinsu Zamfara, da Kebbi kuma, tashe-tashen hankula da auren wuri ya sanya adadin ya kara ninkuwa.

“Yawaitar yaran da ba sa zuwa makaranta ka iya ta’azzara matsalar tsaro a shiyyar, kuma an kiyasta cewa daga cikin yara 18.5 da ba sa zuwa makaranta a Najeriya, miliyan 3.5 sun fito ne daga makiyaya.

Ya kuma bayyana ce an samu fadada makarantun makiyaya a fadin jihohi 36 da babban birnin tarayya daga 3,939 a shekarar 2015, zuwa 4,375 a shekarar 2022.

A nasa jawabin, Daraktan kula da wayar da kan jama’a da ci gaban mata, Dakta Fidelis Ugochukuwu Idoko, ya ce rashin tsaro a yankin Arewa maso Yamma na daga cikin dalilan da suka sanya lamarin ya kara ta’azzara a yankin..