✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yawancin ’yan bindigar da ke addabar mu ba ’yan Najeriya ba ne – Gwamnan Neja

Ya ce an dauko hayarsu ne domin a kassara Najeriya.

Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello ya yi zargin cewa yawancin ’yan bindigar da ke addabar kasar nan ba ’yan Najeriya ba ne.

Ya bayyana hakan ne yana kuma mai jaddada kira ga jama’a da su dage kada su bari su yi nasara wajen kassara kasar.

“Yawancin ’yan bindigar nan bakin haure ne daga wasu kasashen. An dauko hayarsu ne domin a lalata mana kasa. Bafulatani na asali ba zai iya aikata wadannan abubuwan ba,” inji shi.

Gwamnan na jawabi ne lokacin da ya aike da jami’an tsaro 1,000 domin ceto dalibai 136 da aka sace daga makarantar Islamiyyar da ke Tegina a Karamar Hukumar Rafi ta jihar a kwanakin baya.

Hukumomin jami’an tsaron dai sun hada da sojoji da ’yan sanda da sibil difens da kuma ’yan kato-da-gora.

Bayan ziyarar da ya kai wa wasu daga cikin iyayen yaran da aka sace, Gwamna Sani Bello ya ce Gwamnatinsa ta yanke shawarar daukar tsattsauran mataki wajen ganin ta kubutar da su

Ya kuma ce, “Wadannan ’yan bindigar a shirye suke kuma suna da tsari. Ba zai yuwu mu ci gaba da zama mu rungume hannuwanmu ba, dole sai mun dauki tsattsauran mataki wajen kama su tare da masu tsegunta musu bayanai.

“Sun fara da korar manoma daga gonakinsu, sai suka koma kona gonakin, sai kuma satar jama’a wanda ya tilasta mana rufe makarantu.

“Yanzu kuma sun fara kai wa makarantun Islamiyya hari, Allah kadai ya san nan gaba kuma ina za su je.”